An kashe mutum hudu a wata mashaya a Amurka

Asalin hoton, Getty Images
An kashe mutum hudu a wata mashaya a birnin Kansas da ke tsakiyar-yammacin Amurka .
'Yan sandan birnin sun shaida cewa mutane biyar sun raunata lokacin afkuwar lamarin, sai dai ba su bayyana takamaiman inda lamarin ya faru ba.
'Yan sandan sun shaida wa BBC cewa wanda ake zargi dan asalin kasar Spaniya ne kuma ya gudu bayan da abin ya faru.
Babu cikakken bayani dangane da inda wanda ake zargi da kisan yake, ba a san kuma dalilin da yasa ya aikata laifin ba.
Duk da cewa 'yan sanda basu bayyana inda lamarin ya faru ba, kafafen yada labarai na birnin sun ruwaito cewa an yi amfani da bindigar hannu domin kai hari a wata mashaya da ake kira Tequila da ke birnin Kansas.
Wannan na zuwa ne makonni kadan bayan wasu hare-hare har biyu da aka kai a birnin Texas na Amurka inda mutane 44 suka rasa rayukansu.
A 2019, an kai shigen irin wadannan hare-haren kusan 40 a Amurka.
Shagon sayar da makamai na Walmart, wanda ake ganin shi ne ya fi ko wane girma a kasar ya bayyana cewa zai daina sayar da wasu samfuran harsasai da ake amfani da su wajen aiwatar da irin wadannan hare-haren da kananan bindigogi.









