Abba Gida-Gida ya sha kaye a kotu, Buhari ya tafi Afirka ta Kudu: Hotunan Najeriya cikin makon nan

Hoton cikin ginin makarantar Daru Imam Ahmad Bun Hambal a ranar 27 ga watan Satumban 2019
Bayanan hoto, Wannan shi ne ginin makarantar Daru Imam Ahmad Bun Hambal da ke Kaduna inda hukumomi suka kubutar da daruruwan mutane da ake zargin an azabtar da su. An kwashe kwanaki labarin yana jan hankalin duniya. Ranar Lahadi muka wallafa wannan hoto a ci gaban labarin.
An wallafa
Ranar Talata aka yi bikin cikar Najeriya shekara 59 da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallakar Birtaniya. Wannan hoton wasu daga cikin sojojin kasar ne suke faretin ban-girma a fadar shugaban Najeriya da ke Abuja domin tunawa da zagayowar ranar samun mulkin-kan

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

Bayanan hoto, Ranar Talata aka yi bikin cikar Najeriya shekara 59 da samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallakar Birtaniya. Wannan hoton wasu daga cikin sojojin kasar ne suke faretin ban-girma a fadar shugaban Najeriya da ke Abuja domin tunawa da zagayowar ranar samun mulkin-kan
Ranar Laraba Shugaba Muhammadu Buhari ya kama hanyar tafiya Afirka ta Kudu tare da wasu gwamnonin kasar, ciki har da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano da Gwamna Simon Lalong, wadanda kotun sauraren kararrakin zabe suka amince da nasarar da suka yi a zaben watan Maris na 2019

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

Bayanan hoto, Ranar Laraba Shugaba Muhammadu Buhari ya kama hanyar tafiya Afirka ta Kudu tare da wasu gwamnonin kasar, ciki har da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano da Gwamna Simon Lalong, wadanda kotunan sauraren kararrakin zabe suka amince da nasarar da suka yi a zaben watan Maris na 2019...
Sai dai ko da yake hukuncin bai yi wa jam'iyyar PDP dadi ba kuma tuni ta sha alwashin daukaka kara, amma a wannan hoton shugaban jam'iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas(hagu) da kuma na PDP, Rabi'u Sulaiman Bichi sun sha hannu a wajen kotun.
Bayanan hoto, Sai dai ko da yake hukuncin bai yi wa jam'iyyar PDP dadi ba kuma tuni ta sha alwashin daukaka kara, amma a wannan hoton shugaban jam'iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas(hagu) da kuma na PDP, Rabi'u Sulaiman Bichi sun sha hannu a wajen kotun.
Alagba

Asalin hoton, Daily Trust

Bayanan hoto, Ranar Laraba, hukumomi a birnin Ogbomoso na jihar Oyo suka bayar da labarin mutuwar kunkuru mafi tsawon shekaru a duniya mai suna Alagba. An ce kafin mutuwarsa, kunkurun, wanda ke da shekara 344, yana iya magance larurori.
Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaba Cyril Ramaphosa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ranar Alhamis, Shugaba Buhari ya shaida wa takwaransa na Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa cewa bai ji dadin hare-haren kin-jinin-baki da 'yan kasarsa suka kai wa wasu 'yan nahiyar Afirka, cikin har da 'yan Najeriya, kwanakin baya ba.
Sarkin Nguru da ke jihar Yobe, mai martaba Alhaji Mustapha Ibn Mai Kyari(hagu) ya kai ziyara ga ministan sadarwa, Isa Ali Pantami a ofishinsa da ke Abuja ranar Juma'a.

Asalin hoton, Twitter/@ngrcommtech

Bayanan hoto, Sarkin Nguru da ke jihar Yobe, mai martaba Alhaji Mustapha Ibn Mai Kyari (hagu) ya kai ziyara ga ministan sadarwa, Isa Ali Pantami a ofishinsa da ke Abuja ranar Juma'a.