Buhari da Ramaphosa sun tattauna a Afirka ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images
Shugabannin manyan kasashen Afirka biyu, Najeriya da Afirka ta Kudu sun gana a lokacin da ake farfadowa daga tashin hankalin hare-haren kin jinin baki da aka yi a birnin Johannesburg wanda ya fi shafar 'yan Najeriya.
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ne mai masaukin Shugaba Muhammadu Buhari a birnin Pretoria kuma ana fata shugabannin biyu za su kawo karshen tashin hankalin sannan su mayar da hankali kan hadin kai a fannin tattalain arzikin kasashen biyu.
A cewar shugaban Najeriya "Kasashen namu biyu sun amince wajen magance matsalar dangantakarmu musamman tsakanin mutane zuwa mutane, da kuma hare-haren da ake kaiwa mutanen da ba 'yan kasa ba har da 'yan Najeriya - wanda muka yi Allah-wadansa.
Shi kuwa shugaban Afirka ta Kudu sai ya ce "A shirye muke domin mu magance matsalolin da suke damun mutanenmu na matsalolin talauci da rashin aikin yi da shan kwayoyi da aikata laifuka da kuma ci rani. A shirye muke mu tabbatar da doka a kan dukkanin masu aikata laifuka ko 'yan wace kasa ce domin tabbatar da cewa an hukunta su."
Ma'aikatan BBC a biranen Legas da Johannesburg sun duba mana yadda kasashen biyu ke kallon juna.

Kishoyi kuma abokai
Daga Mayeni Jones, BBC News a Legas
Ana iya cewa akwai dadadden kishi tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu. 'Yan Najeriya da dama na ganin Afirka ta Kudu a matsayin kishiyarsu a bangaren wasanni da al'ada da tattalin arziki.
Su ne kasashe biyu da suka fi tattalin arziki a nahiyar Afirka, inda a lokuta daban-daban daya kan yi wa dayar fintinkau.
A fagen al'ada, kide-kiden Najeriya ta mamaye duniyar wake-wake a duniya kuma mawakanta ba daga cikin mafi shahara a mawakan Afirka a duniya.
Kasar ita ce kan gaba a masana'antar waka a nahiyar kuma an yi kiyasin cewa nan da shekarar 2020, masana'antar za ta kai kimar dala miliyan 86 ko fam miliyan 70.
Amma duk da haka, masana'antar waka a Afirka ta Kudu ta fi girma, inda aka yi kiyasin cewa a shekarar 2020 kimarta za ta kai dala miliyan 178.
Abin kawai da ya rage yanzu shi ne, ku zauna da masu sha'awar kwallon kafa a lokacin wasa tsakanin tawagogin kasashen biyu na Super Eagles da Bafana Bafana, don sanin zurfin yadda kasashen biyu ke adawa da juna.

Asalin hoton, Getty Images
A tarihi, Najeriya ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da tallafin diflomasiyya ga fafutukar yaki da wariyar launin fata ta Afirka ta Kudu.
Kuma tun bayan da kasashen biyu suka koma tsarin dimokuradiyya, sun ci gaba da zama kawaye a fannin tattalin arziki.
Wasu daga cikin manyan kamfanonin da ke aiki a Najeriya, ciki har da kamfanin waya na MTN da rukunin shagunan sayar da kayan masarufi na Shoprite da kamfanin tauraron dan Adam na Multichoice - duka na Afirka ta Kudu ne.
Banbancin tattalin arzikin Najeriya da Afirka ta Kudu
Amma duk da cewa ya cancanta kasashen biyu su yi kishi, 'yan Najeriya da dama na nuna takaicinsu kan abin da suke cewa 'yan Afirka ta Kudu na da son nuna komai nasu ne.
Hare-haren kin jinin baki da aka yi a baya a Afirka ta Kudu a 2008 da 2015 da suka shafi 'yan cirani daga kasashen Afirka masu fama da talauci, sun sa 'yan Najeriya da yawa ganin cewa 'yan Afirka ta Kudu na nuna bacin ransu ga mutanen da basu cancancin hakan ba.
An nuna haka a titunan Legas da kan shafukan sada zumunta a hare-haren watan jiya a birnin Johannesburg da wasu biranen.
'Yan Najeriya sun garzaya shafukan sada zumunta da gidajen rediyo don bayyana bacin ransu kan cewa, ana kai wa wasu 'yan Afirkan da suke neman kudi a Afirka ta Kudu.
A shirye-shiryen talabijin a tauraron dan Adam, masu gabatar da shirye-shiryen sun yi ta sukar hare-haren.
A ganinsu, idan 'yan Afirka ta Kudu sun fi kwazo, me ya sa sauran 'yan Afirka suke samun kudi ta hanyarsu. Kuma ma, ai kamata ya yi su nuna bacin ransu ga fararen fata 'yan kasarsu da suka mamaye masu tattalin arziki.
Wannan bacin ran ya bazu har zuwa titunan biranen Najeriya.
Matasa, wanda ake zargi suna neman ramuwa, bayan bidiyo da hotunan karya da suka rude su a shafukan sada zumunta, sun fara balla shaguna tare da sace kayan ciki kuma daga bisani suka kona sana'o'in Afirka ta Kudu.
Gwamnatocin biyu sun ja kafa wajen bayyana gaskiyar adadin mutanen da suka mutu a rikicin.
Sun saki jiki dangane da irin fushin da farfagandar intanet ke iya haifarwa.
Banbancin tattalin arzikin 'yan Najeriya da Afirka ta Kudu
Sai dai wasu masu sharhi na ganin cewa yawan marasa aikin yi a Najeriya, wanda ya ninka sau uku a shekaru biyar da suka gabata na da nasaba da abin da ya faru.
Rashin aikin yi ya yi kamari a tsakanin matasan kasar kuma da yawa daga cikin wadanda suka balla shagunan sun kai wa snaa'o'in 'yan Najeriya hari, kuma haka ya nuna cewa babu mamaki manufarsu ta fi karfin rama harin kin jinin baki da aka yi a Afirka ta Kudu.
Don haka, a iya cewa Najeriya da Afirka ta Kudu na da wani abu guda iri daya: tattalin arzikinsu ya ragu a 'yan shekarun nan inda hakan ya haifar da kin jinin jam'iyyu masu mulki. Wannan ya jawo bacin rai da tashe-tashen hankula da suka bai wa hukumomi mamaki.
Don haka ne Shugaba Ramaphosa da Shugaba Buhari suke son su kawo karshen matsalar kin jinin baki, sannan su nemo hanyoyin hadin kai wajen farfado da tattalin arzikin kasashensu.

Dangantakarmu ta soyayya da kiyayya
Daga Milton Nkosi, BBC News a Johannesburg
'Yan Afirka ta Kudu na kallon 'yan Najeriya a matsayin kishiyoyinsu amma kuma 'yan uwansu.
Akwai dangantakar soyayya da kiyayya da ta dade tsawon shekara da shekaru. Duka na ganin suna da wani matsayi a tarihin Afirka kuma duka na alfahari da kasancewa manyan tattalin arzikin nahiyar.
'Yan Najeriya da yawa sun zo Afirka ta Kudu lokacin da aka koma tsarin demokradiyya a 1994 bayan da aka kawo karshen wariyar launin fata na apartheid.
Amma an samu sauyi kuma 'yan Najeriya na ganin wasu 'yan Afirka ta Kudu sun yaudaresu ta yadda suke yi masu.

Asalin hoton, Getty Images
Akwai munanan halaye da yawa da ake alakanta 'yan Najeriya da su kamar safarar miyagun kwayoyi da mutane da damfara ta intanet. Duk da cewar aikata manyan laifuka ya karu a Afirka ta Kudu, 'yan kasar na hanzarin zargin baki da aikata su.
Wata matsalar ita ce karuwar coci-coci- wanda fastocin 'yan Najeriya ne - inda abubuwan da suke koyawa na da mishkila.
Shari'ar mai wa'azi dan Najeriya Timothy Omotoso da aka nuna a talabijin, wanda aka zarge shi da cin zarafiun mabiyansa, ya girgiza mutane a nan kuma ya kara rura wutar kiyayyar baki.
Mista Omotoso ya musanta zargin.
Akwai kuma yawan mutane masu neman aiki, ba wai ma'aikata marasa kwarewa kawai ba.
A kasashen duniya, 'yan Najeriya na daga cikin wadanda ke samun takardun kammala karatu a manyan jami'o'in duniya irinsu Harvard da Yale da Oxford da kuma Cambridge.
Wasu 'yan Afirka ta Kudu na jin takaicin yadda baki ke da gurbi a kamfanonin da ke biyan albashi mai tsoka.
Suna ganin ba a yi adalci ba saboda suma sun kammala karatu a jami'o'in kasarsu da ke da kyau, amma an banzatar da kwarewarsu.
Cikin hushi, wasu sun bayyana cewa 'yan Najeriyar masu ilimi na iya bayar da gudummawa mai amfani a kasarsu inda ake bukatarsu, maimakon zuwa kasashen waje su mamaye manyan ayyukan daga hannun 'yan Afirka ta Kudun da suka cancanci su yi ayyukan.
Yawan mutanen Najeriya da Afirka ta Kudu
Amma dangantaka tsakanin kasa da kasa, da alama tana da kyau. A farkon watan nan Shugaba Buhari ya gode wa jakadan Afirka ta Kudu Jeff Radebe bisa zuwan da yayi Najeriya don ya bayar da hakuri kan tashin hankalin na kwanan nan.
Kuma wannan ya faru ne duk da 'yar tangardar da aka samu idan Najeriya ta ci tarar kamfanin MTN na Afirka ta Kudu dala biliyan 5, amma daga baya aka rage bayan tattaunawa.
Jami'ai a nan, musamman mambobin jam'iyyar ANC mai mulki sun yi farin ciki da tallafin da Najeriya ta bai wa kasarsu lokacin fafutukar neman 'yancin bakake.
Manyan shugabanni sun yi gudun hijira na rajin kai daga mulkin farar fata 'yan tsiraru. Wasu daga cikinsu, har da Shugaba Thabo Mbeki wanda ya zauna a Najeriya, ba sa jin dadi idan 'yan uwansu 'yan Afirka ta Kudu suka kai wa wasu 'yan Afirka hari.
Suna jin kunya da abin da suke kira nuna kin jinin 'yan Afirka.
Kamar yadda Shugaba Ramaphosa ya shaida min a wata tattaunawa ta ba-zata cikin watan da ya gabata cewa abin kunya ne ga 'yan Afirka ta Kudu.












