Gimbiya Meghan ta maka jaridar Mail a kotu

Asalin hoton, EPA
Gimbiyar Sussex ta kai karar jaridar Mail a gaban kuliya dangane da wani labari da ta buga game da ita.
Gimbiyar ta dauki matakin ne saboda wata wasikarta da jaridar ta buga ta haramtacciyar hanya.
A cewar Yariman Sussex Harry, shi da Gimbiya an kai su bango ne saboda irin "farfagandar" da ake yi masu.
A ranar Lahadi kakakin jaridar ya bayyana cewa jaridar tana nan a kan labarin da ta buga kuma za ta kare kanta a gaban kotu.
Masu kare Gimbiyar sun zargi jaridar da kokarin bata mata suna.
Lauyoyin Gimbiyar sun kai karar kamfanin jaridar a kan amfani da bayanan sirrin mutanen da shiga hakkinsu da kuma saba wa dokar kariyar kutse a kan bayanan mutane ta shekarar 2018.
Lamarin ya taso ne bayan da jaridar Mail a ranar Lahadi ta buga wasikar da Meghan ta rubuta wa mahaifinta, Thomas Markel da hannunta, bayan da suka yi aure da Yarima Harry a 2018.







