BBC ta kaddamar da sabon shiri don masu nakasa

An wallafa

Shugaban BBC Tony Hall, ya sanar da wani sabon shiri ga 'yan jarida masu lalurar nakasa mai suna "Aim High" a kasar Kenya.

An bullo da shirin ne bayan wasu sabbin tsare-tsaren horar da 'yan jaridar Afirka masu tasowa.

Tony Hall, wanda ke ziyara a ofishin BBC a Kenya, ya ce sabon shirin zai bai wa 'yan jarida uku masu nakasa damar aiki tsawon wata uku daga watan Afrilun 2020.

'Yan jaridar za su yi aiki a ofishin na Nairobi tare da ma'aikata daban-daban daga sassan Afirka, kuma za su yi aiki a talabijin da bangaren intanet.

Tony Hall ya ce "BBC ta dade da burin kawo labarai daga Afirka, inda take kai labarai ga fiye da mutum miliyan 100 duk mako."

Ya ci gaba da cewa "Muna so mu inganta da kuma tabbatar da aikin jarida na kashin kai a nahiyar, da kuma tallafa wa wadanda ba a cika bai wa damar bayar da labarai ba.

"Mun san cewa abu ne mai wuya ga mutane masu nakasa su samu dama a bangaren aikin jarida.

"Shirin Aim High zai bai wa 'yan jarida masu nakasa horo da ilimin aiki da shawarwari, kuma ina kira ga mutane da su nemi wannan damar."

Za a fitar da karin bayani nan gaba kan yadda za a shiga shirin.

Tony Hall dai ya je Kenya ne don murnar nasarorin da BBC ta samu a Afirka.

Kafar yada labaran na aiki ne a harsuna 13 a fadin nahiyar kuma ta kaddamar da sabbin shirye-shiryen talabijin 20 a watanni 18 da suka gabata ciki kuwa har da shirin Africa Eye mai binciken kwakwaf.