Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dan Uganda ya lashe kyautar Komla Dumor ta 2019
Dan jaridan kasar Uganda mai binciken kwakwaf kuma mai gabatar da labarai, Solomon Serwanjja, ya lashe kyautar Komla Dumor ta BBC a 2019.
Serwanjja yana gabatar da labarai a gidan talbijin na kasar Uganda wato NBS TV, inda yake hira da baki da dama a shirin nasa.
Ya yi rahotanni na gani da na fada da suka sanya ya samu kyaututtuka da suka hada da rahoton da ya yi wa sashen bincike na BBC Africa Eye a kan yadda ake sayar da magungunan da ya kamata likita ya rubuta wa mutum, ba bisa ka'ida ba a kasar.
An kirkiro wannan kyauta ne domin karrama Komla Dumor wanda mai gabatarwa ne a BBC bayan ya yi mutuwar farad-daya a 2014 yana mai shekara 41.
Serwanjja ne dan jarida na biyar da ya lashe kyautar ta Komla bayan Waihiga Mwaura da Amina Yuguda, da Didi Akinyelure da kuma Nancy Kacungira.
Sakamakon lashe wannan kyauta, Serwanjja zai kwashe wata uku a ofishin BBC na London domin sanin makamar aiki daga wurin kwararrun 'yan jarida.
Har wa yau, Serwanjja zai samu damar koma wa nahiyar Afirka domin hada rahotanni a kan nahiyar.