'Tarbiyyantar da yara ake a makarantar Kaduna ba azabtarwa ba'

An wallafa

Latsa wannan alamar lasifikar da ke sama domin sauraron hirar

Kungiyar malaman makarantun Islamiyya karkashin kungiyar Izala ta Rigasa da ke birnin na Kaduna ta yi Allah-wadai da kai wa abin da suka kira 'makarantar tarbiyya' samame.

A wata hira da Haruna Ibrahim Kakangi, Mallam Aliyu Adam, shugaban kungiyar malaman makarantun Islamiyya karkashin kungiyar Izala ta Rigasa da ke birnin na na Kaduna ya ce suna goyon baya ga abubuwan da ake yi a cibiyar.

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna dai ta bayyana wurin da na 'bautar da bil adama' ne, inda akasarin mutanen ciki suke daure da sarka ko kuma mari.

Tun farko dai rundunar 'yan sandan ta ce mutanen da aka kubutar sun kai 300 zuwa 500 amma yanzu mutane 190 aka mika wa Ma'aikatar Ayyukan kyautata Rayuwar bil Adama da Zamantakewa ta jihar.

Wasu hotunan da aka samu da ke nuni da azabtarwa: