‘Yan bindiga sun kai hari kan sansanin sojin Amurka

Baledogle airport in 1992 - payable single online use only

Asalin hoton, Alamy

An wallafa

Masu ikirarin jihadi sun kai hari a wani sansanin horar da sojojin Somaliya inda dakarun Amurka ke ba su horo.

Mazauna yankin Lower Shabelle sun shaida cewa sun ji karar harbin bindiga da kuma fashewar bam a filin jirgin Baledogle.

Tuni dai kungiyar al-Shabab ta dauki nauyin kai harin, inda tayi amfani da mota mai dauke da nakiya ta fasa kofofin shiga sansanin kafin mayakanta suka afka ciki.

Sai dai jami'an tsaro sun shaida cewa sun kora mayakan al-Shabab din.

Map

A wata sanarwa da kungiyar al-Shabab din ta fitar ta bayyana cewa ita ce ta kai harin kuma ana ci gaba da gwabzawa.

Sanarwar ta ce ''Bayan mun kutsa cikin sansanin mai matukar tsaro, mun tunkari sojoji inda muka fara musayar wuta.''

Sansanin horaswar na da nisan kilomita 100 daga babban birnin kasar Mogadishu.

Sansanin na dauke da dakarun sojoji na musamman na Amurka da na Uganda da kuma na Somaliya.

A wani bangaren kuma, ma'aikatar tsaron Italiya ta bayyana cewa an kai harin bam ga ayarin motocin sojoji na Italiya a Mogadishu.

Amurka ta kara kaimi wajen kai hari ga kungiyar al-Shabab wacce ke da alaka da al-Qaeda tun bayan zaman Donald Trump shugaban Amurka.

Jami'ai a Mogadishu sun bayyana cewa kungiyar al-Shabab ta kara yawan hare-haren da take kaiwa a matsayin ramuwar gayya kan hare-hare na sama da ake kai musu.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta shaida cewa al-Shabab na da iko da sassa daban-daban na Somaliya, kuma kungiyar na iya kai manyan hare-hare na kunar bakin wake da amfani da bama-bamai da manyan makamai.