Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tsohon shugaban Faransa Jacques Chirac ya mutu
Jacques Chirac, tsohon shugaban Faransa, wanda ya yi fama da zarge-zargen cin hanci da rashawa bayan ya sauka daga mulki, ya mutu yana da shekara 86.
Surukinsa ya shaida wa kamfanin dillancin labaria na AFP cewa "Shugaba Jacques Chirac ya mutu a safiyar nan cikin kwanciyar hankali zagaye da iyalansa."
Mr Chirac ya yi shugabancin Faransa sau biyu kuma shi ne shugaban da ya shugar da kasarsa cikin kungiyar kasashen turai da ke amfani da kudi bai-daya.
Daya daga cikin manya-manyan sauye-sauyen da ya kawo shi ne rage wa'adin shugabancin kasa daga shekara bakwai zuwa shekara biyar.
Ana kallon sa a matsayin mutumin da ya yi adawa da mamayar da Amurka ta yi wa Iraki a shekarar 2003.
Ya yi mulki a matsayin shugaban kasa daga 1995 zuwa 2007, kuma tun daga nan ne yanayin lafiyarsa ya rika tabarbarewa.