'Tattalin arzikin Najeriya zai durkushe in har...'

Abubakar Malami, babban lauyan gwamnatin Najeriya kuma ministan shari'a

Asalin hoton, TWITTER/@MALAMISAN

Bayanan hoto, Abubakar Malami ya ce ba za su mika wuya ba sai sun ga karshen inda shari'ar za ta kai
An wallafa

Tattalin Najeriya ka iya durkushewa, matukar gwamnatin kasar ta bai wa wani kamfanin Birtaniya sama da dala biliyan 9—kudin da wata kotun London ta bayar da umarni a ba shi.

Wani masanin shari'a dan Najeriya, Barista Audu Bulama Bukarti, wanda ya yi wannan gargadi, ya ce kulla yarjejeniya ko yin sulhu su ne kadai maslaha ga takaddamar da ake yi tsakanin gwamnatin kasar ta Najeriya da kamfanin na iskar gas mai suna Process & Industrial Development Ltd.

"Wadannan makudan kudade ne.... Sun kai [kashi] daya bisa biyar na gaba daya duliyar Najeriya da ke [asusun ajiya na] kasashen waje", inji Barista Bukarti, wanda ya kara da cewa, "saboda haka ni ina ga mafita ga gwamnati [ita ce] a zauna a yi yarjejeniya, a yi sulhu, su bar maganar dala biliyan 9 a duba wani abu da za a iya ba su a ba su, a bar wannan maganar".

Kotun ta London ta bayar da wannan umarni ne, wanda bai yi wa hukumomin Najeriya dadi ba, bayan suka gaza aiwatar da wani hukuncin da tun farko ya bukaci kasar ta biya P&ID dala miliyan 800 sakamakon rashin cika sharadin wata yarjejeniyar sarrafa iskar gas da bangarorin biyu suka cimma a shekarar 2010.

Bututan mai da iskar gas

Asalin hoton, Getty Images

A cewar lauyan, tunkarar kotun ta Ingila da ta bayar da umarnin ba zai gamsar da ita ba, saboda babu wata kara da aka daukaka kan umarnin da zai bai wa ita Najeriyar damar shigar da korafinta ga kotun.

"Za su iya zuwa Kotun Daukaka Kara, daga nan su je Kotun Koli, amma mganar da nake yi ko sun je Kotun Daukaka Kara magana za su yi cewa a dakatar da zartar da hukunci, ba maganar hukuncin ba ne saboda hukuncin ba a nan aka yi shi ba", inji Barista Bukarti.

A ranar Alhamis ne jami'an gwamnatin Najeriyar za su bayyana a gaban kotun don kalubalantar babban hukuncin, matakin da Barista Bukarti ke ganin ya zo a makare ganin irin tsawon lokacin da Najeriyar ta dauka tun shekarar 2013 ba tare da wani yunkuri na nuna rashin amincewa da umarnin kotun ba.

Ministan shari'ar Najeriya, Abubakar Malami shi ke jagorantar jami'an kasar zuwa kai korafin gaban kotun ta London.

A wata hira da BBC, Malami ya ce a shekarar 2010 ne kamfanin ya gabatar da bukatarsa ta kafa masana'antar iskar gas sai dai ya ce ba a shigar da kamfanonin da suke da alhakin bai wa shi kamfanin P&ID iskar gas din ba cikin yarjejeniyar, abin da ya sa kamfanin da gwamnatin Najeriya suka kulla yarjejiniyar tun da farko.

Ma'aikatan mai da iskar gas

Asalin hoton, Getty Images

Ya ce kamfanin ''bai nemi kasa ko wuri inda ya kamata ya yi kamfanin ba, bai gina masana'antar ba, bai kuma kawo ko taro ba da nufin yin wannan aiki a Najeriya ta wannan fuska.

"Amma a shekarar 2014, sai kotun London ta yi hukuncin cewa gwamnatin Najeriya ta sabawa yarjejeniyar saboda ta gaza samar da iskar gas da kamfanin ke bukata.''

Shi dai ministan ya ce girman kudin da kotun ta bai wa kamfanin ikon kwacewa daga Najeriya ya kai kashi 30 cikin 100 na kasafin kudin kasar na wannan shekarar.

Wanda kudin da ya fi karfin kudaden da aka ware jumulla domin kashewa a bangaren lafiya da ilimi da tsaro a shekarar 2019.

"Ba za mu bayar da kafa ta tattaunawa ta fuskar bayar da taro da kobo ba," in ji Ministan shari'ar.

Malami ya kara da cewa sam ba su yarda da umarnin kotun ba na raba Najeriya da kadarorinta inda ya bayyana kudirinsu na ganin sai sun ga abin da zai ture wa buzu nadi kan batun.