China ta fara mamaya a kasashen Turai

'Yan sandan Serbia na dauki-ba-dadi da masu zanga-zanga

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, 'Yan sandan China za su rika aikin tsaro ne tare da 'yan sandan kasar ta Serbia
An wallafa

Jami'an 'yan sanda na China sun fara wani aikin sintiri na hadin-guiwa da takwarorinsu a babban birnin kasar Serbia, Belgrade, domin bunkasa harkar yawon bude idanu a kasar, in ji gwamnati.

Wannan na nuna irin tasirin da ake ganin China na yi a harkokin Serbia a cikin wannan lokaci.

Ga hukumomin kasashen biyu dai, wannan a cewarsu ba wani abu ba ne da yake da wata manufa illa batu na samar da cikakken tsaro domin bunkasa yawon bude idanu, illa iyaka, ganin yadda ake samun karuwa shekara bayan shekara ta masu zuwa kashe kwarkwatar idanunsu daga China a birnin na Belgrade.

Ministan harkokin cikin gida na Serbia, Nebojša Stefanovic, ya ce masu sintirin za su taimaka wa 'yan China masu yawon bude idanu.

Wani masanin harkokin tsaro da ke birnin na Belgrade ya ce ba shakka masu aikin sintirin za su taimaka wa 'yan yawon bude idon na China, amma ya yi suka game da rashin bayyana ainahin iya ikon da 'yan sandan na China suke da shi a kasar.

Masu zanga-zanga a Serbia

Asalin hoton, EPA

Kididdiga ta nuna yadda aka samu karuwar masu yawon shakatawar da kashi 40 ciki dari a shekara.

Wanda hakan ana ganin ya ksance ne kusan saboda damar shiga kasar ga 'yan China ba tare da takardar izini, ba viza.

Bayan karuwar masu yawon bude idanun akwai kuma tudadar masu harkokin kasuwanci ma zuwa kasar ta yankin Balkan.

Kamfanonin China tuni sun karbi gudanarwar ayyukan samarwa da sarrafa tama da jan-karfe na Serbia.

Sannan bashin da gwamnatin China ta ba wa kasar shi ne har ya sa ta bijiro da sabon aikin jirgin kasa mai dan-karen gudu, tsakanin Belgrade da Budapest, wato babban birnin Hungary.

'Yan sanda a zanga-zangar Hong Kong

Asalin hoton, Getty Images

Shigar Chinan harkokin tsaron kasar ta Serbia, ya kai ga bunkasa matakan tabbatar da tsaron ta hanyoyi na zamani, kama daga amfani da fasahar gane fuskar mutum musamman mai laifi, zuwa samar da kananan jiragen sama marassa matuka na soji.

Bayan aikin sintirin 'yan sandan na hadin guiwa, a babban birnin, Belgrade, akwai kuma wasu birane biyu da za a yi hakan su ma.

Jakadan China a Serbia ya ce jami'an 'yan sandan nasu za su kasance jakadu na kawance da sada zumunta.