Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kwamitin tattalin arziki: "Buhari bai rage wa Osinbajo karfin iko ba"
Latsa alamar lasifika da ke sama domin sauraron hirar:
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya kaddamar da majalisar bai wa shugaban kasa shawara kan tattalin arziki.
Hakan ya biyo bayan rushe kwamitin tattalin arzikin kasar, wadda mataimakin shugaban kasar Professor Yemi Osinbajo ke jagoranta.
Yayin da wasu ke cewa sambarka, wasu dai na kallon matakin a matsayin yunkurin rage ikon mataimakin shugaban kasar.
Amma a tattaunawarsu da Ibrahim Isa, mai taimaka wa shugaban kasar kan harkar yada labarai, Mallam Garba Shehu ya ce ba haka lamarin yake ba.
Garba Shehu ya ce an kafa wannan kwamiti ne kamar yadda ake da masu bayar da shawara a fannoni daban-daban na harkokin kasa.
Kuma a cewarsa ana sa ran wannan kwamiti zai taimaka wajen magance irin matsalolin da tattalin arzikin kasar ke fama da su.
Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce kwamitin tsaro da ake da shi a baya ya yi bakin kokarinsa a bangaren tattalin arziki.
Amma a acewarsa gwamnati ta ga cewa lokaci ya yi da za a sauya dabara.