Shugaban Afghanistan ya tsalle rijiya da baya a harin bam

Asalin hoton, Reuters
Akalla mutum 24 ne suka mutu sannan mutum 31 suka jikkata sakamakon wani harin kunar baki wake da aka kai wurin wani gangamin yakin neman zabe a kasar Afghanistan.
Harin ya afku ne a lardin Parwan da ke arewacin babban birnin kasar Kabul, lokacin da shugaba Ashraf Ghani ke dab da ya fara yin jawabi a gangamin.
Wani harin bam din a kusa da ofishin jakadancin Amurka a birnin na Kabul, ya yi sanadiyyar mutuwar mutum uku.
An dai ce maharin wanda yake kan babur ya tayar da bam din ne a wani shinge da aka kafa a wurin taron gangamin kamfe din.
Ma'aikatan lafiya sun ce akwai kananan yara daga cikin wadanda suka jikkata.
'Yan kungiyar Taliban sun ce su ne suka kai harin guda biyu. Kungiyar dai na ci gaba da kai hare-hare a dai-dai lokacin da take ci gaba da zaman sulhu da ake yi a kasar.
To sai dai a farkon watan nan Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana tattaunawar da ake yi da kungiyar da "Wadda ba ta da amfani".
Kungiyar Taliban dai ta ki amince wa ta tattauna da gwamnatin kasar inda kuma ta sha alwashin hana ruwa gudu dangane da zaben shugaban kasa da za a yi ranar 28 ga watan Satumba.

Wasu alkaluma da BBC ta samo na nuna cewa akalla mutum 74 ne ke mutuwa a kulluyaumin a watan Agustan da ya gabata sakamakon hare-hare a kasar.
Ranar da ta fi muni ga fararen hula a kasar ita ce 18 ga watan Agusta, lokacin da mutum 112 suka mutu da suka hada da 92 da bam ya tashi da su a wani wurin taron biki.
Alkaluman sun nuna cewa adadin fararen hula da suka mutu a rikicin Afghanistan a watan na Agusta ya fi wadanda suka hallaka a Syria da Yemen idan aka hada.
Mutum 2,300 ne aka kashe a kasar cikin watan Agustan, daga cikin su kuma guda 473 fararen hula ne, yayin da sauran kuma ko dai mayakan Taliban ne ko kuma jami'an tsaro, kamar yadda binciken ya nuna.
A watan Yunin 2019 ne aka ayyana Afghanistan a matsayin kasar da ake tashin hankali a duniya.












