Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zaben Tunisiya: Mutum miliyan 7 za su jefa kuri'a a Tunisiya
A ranar Lahadi ne 'yan Tunisiya za su kada kuri'ar zaben sabon shugaban kasa, makwanni shida bayan rasuwar Shugaba Beji Caid Essebsi.
'Yan takara 26 ciki har da mata biyu za su fafata a zaben, shekaru 8 kenan bayan kadawar guguwar sauyi a kasashen Larabawa wacce ta faro daga Tunisiya.
Shugaban Majalisar kasar Muhammad Annaceur shi ke jan ragamar kasar a matsayin shugaban riko.
Idan har babu dan takarar da ya yi nasara a zagayen farko, za a zabi 'yan takara biyu da suka fi sauran yawan kuri'u don su fafata a zagaye na biyu.
Ana ganin wannan zaben zai zama kamar wani zakaran gwajin dafi ga kasashe masu tasowa a fannin dimokradiyya.
Mista Essebsi ne ya fara lashe zabe a kasar a 2014 inda ya samu shaida wajen wanzar da zaman lafiya a kasar a kusan shekaru biyar da ya shafe yana mulkin kasar.
Ya rasu yana da shekaru 92, wanda kafin rasuwarsa shi ne shugaba mafi tsufa kan karagar mulki a duniya.
A kwanakin baya kafin rasuwarsa, ya tabbatar da cewa ba shi da ra'ayin kara tsayawa takarar shugabancin kasar.
Wani abin al'ajabi da ya faru a kasar a ranar zaben shi ne an wayi gari da labarin mutuwar uwar gidan Mista Essebsi wato Chadlia Saida Farhat inda dansu ya sanar da mutuwar a shafin Facebook a daidai lokacin da ake shirin fara jefa kuri'a a kasar.
Me ya sa zaben ke da muhimmanci?
Kasar ta sha yabo kwarai da gaske a matsayin kasar da ta tsaya da gindinta a kan turbar dimokradiyya daga cikin kasashen larabawa da suka yi bore bayan kadawar guguwar sauyi.
Boren ya fara ne daga Tunisiya sa'annan ya fadada zuwa kasashen da ke Gabas Ta Tsakiya da kuma Arewacin Afirka.
Daya daga cikin abin da ya sa aka yaba da dimokradiyyar kasar shi ne kasar ta shirya muhawara tsakanin 'yan takarar shugabancin kasar inda aka yada muhawarar kai tsaye a tashosin talabijin na kasar.
Wannan ne karo na farko a tarihin kasar da aka taba yin haka.
Sai dai a tafiyar dimokradiyyar kasar an samu tsaiko nan da can domin kuwa a 'yan shekarun nan, kasar ta sha fama da hare-hare na 'yan kungiyar da ke ikirarin jihadi, hakazalika an samu matsi na tattalin arziki da kumar rashin ayyukan yi a kasar.
A 2018 ne 'yan kasar suka fito kan tituna suka gudanar da zanga-zanga kan tsare-tsaren gwamnatin kasar da suka janyo matsi ga tattalin arziki.