An tantance gawarwaki 44 da aka gano a wata rijiya a Mexico

A digger uncovering the mass grave in Jalisco, Mexico, earlier in September

Asalin hoton, AFP

An wallafa

Masana kimiyya da ke binciken kwakwaf kan kwayoyin halitta sun tantance gawarwaki 44 da aka binne a cikin wata rijiya a jihar Jalisco da ke Mexico

An gano gawarwakin ne cikin bakaken jakunkuna 119 a wajen birnin Guadalajara a cikin rijiyar.

Tun asali an gano gawarwakin ne a farkon watan Satumbar bana bayan da mazauna yankin suka fara kokawa kan cewa wari na damun su.

Jihar Jalisco ta yi suna a matsayinta na matattarar gungun masu safara da cinikayyar miyagun kwayoyi a Mexico.

Wannan ne karo na biyu da ake gano gawarwaki a jihar a bana.

Akasarin gawarwakin an daddatsa su, a wannan dalili ne ya sa aka yi kokarin hada sassan jikin gawarwakin domin tantance ainahin mutanen.

Har yanzu bayan hada wasu sassan jikin an kasa tantance asalin mutanen da aka datsa.

Wata kungiya da ke cigiyar wadanda suka bace a jihar ta bukaci gwamnatin jihar da ta kara tura kwararru domin tantance gawarwakin.

Kungiyar ta kuma koka kan cewa masana kimiyyan da ke binciken kwakwaf kan kwayoyin halitta da aka kai su yi binciken ba su da kwarewar da za su tantance gawarwakin.