Kasashen yamma ne ke da alhakin yakin Yemen - MDD

An wallafa

Kwararru daga Majalisar Dinkin Duniya sun ce akwai yiyuwar kasashen Amurka da Burtaniya da Faransa da Iran na da hannu a laifukan yaki da bangarorin da suke goyon baya ke aikatawa a kasar Yemen.

Wani sabon rahoton da MDD ta fitar ya yi gargadin cewa ana iya kama kasashen da laifin taimaka wa masu aikata laifukan yaki.

Manyan kasashen Yamma na tallafa wa gamayyar dakarun da Saudiyya ke jagoranta da makamai da kayan aiki, yayin da Iran ke goyon bayan 'yan tawayen Houthi.

Kwararrun sun ce bangarorin biyu na ci gaba da aikata laifukan yaki ba tare da wata fargaba ba.

Rahoton da kwararrun suka fitar ya tattara bayanai kan laifukan da bangarorin ke aikatawa a rikicin wanda shi ne mafi muni a fadin duniya.

Rahoton ya ce laifukan sun hada da hare-haren da jiragen sama a yankunan fararen hula ke kai wa ba kakkautawa, da harbe-harben kan mai uwa da wabi da azabtarwa da kisan gilla da fyade a cibiyoyin tsare masu laifi da kuma hana kayayyakin agaji kai wa ga mutane.

Rikicin na Yemen da aka kwashe shekara hudu ana gwabzawa ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 7,290 da kuma jefa mutum miliyan 24 - kashi 80 cikin 100 na 'yan kasar - cikin mawuyacin hali na neman kayayyakin biyan bukatu na musamman, cikinsu har da mutum miliyan 10 masu tsananin bukatar abinci.

Tawagar wacce ta kunshi mashahuran kwararru kan rikicin na Yemen sun tattauna sau 600 da shaidun gani da ido da wadanda rikicin ya shafa,

Sannan suka gudanar da nazarin wasu hujjoji da suka tattara daga hannun jama'a da rohoton da suka samu wadanda suke a bayyane, a bangare na biyu na hade da rahoton Hukumar Kare Hakkin Dan'adam ta Majalisar Dinkin Duniya.

Kwararrun sun ce suna da kwararan hujjojin da ke tabbatar da cewa gwamnatin Yemen da gamayyar rundunar tsaro da Saudiyya ke jagoranta da bangaren 'yan tawayen Houthi sun karya dokoki tare da take hakkin jama'a ba tare da an hukunta su ba.

Tawagar kwararrun ta kuma binciki hare-haren da jiragen sama suka kai a yankunan da ke hannun 'yan tawayen Houthi, inda hare-haren suka kashe fararen hula.

Masanan sun ce hare-haren sun haifar da damuwa kan ainihin manufar dakarun gwamnati da kuma kiyaye dokoki da yin taka-tsan-tsan yayin kai hare-hare.

Rahoton ya ce idan har zargin kai hare-hare ba tare da la'akari da abin da zai haifar ba ya tabbata, to hakan na iya zama babban laifi da kuma karya dokokin kasashen duniya.

Ana zargin cewa dukkan bangarorin sun yi amfani da hana juna samun abinci a matsayin dabarar yaki.

Masanan sun bukaci a gaggauta dakatar da dukkan nau'o'in tashe-tashen hankula da ake yi wa fararen hula sannan suka yi kira ga sauran kasashe da su dakatar da samar da makamai ga bangarorin da ke yakar juna a rikicin na Yemen.

Tun a shekarar 2015 aka mamaye birnin Taiz, wanda shi ne gari na uku mafi girma a kasar ta Yemen.

Kwararrun sun jaddada cewa: "Wajibi ne gwamnatoci su dauki dukkan kwararan matakan tabbar da ganin wasu kasashe na kiyaye dokokin duniya na kare hakkin dan Adama.

"Sannan yarjejeniyar cinikayyar makamai da kasashen Faransa da Birtaniya ke cikin kasashen da suka sanya hannu a kai, ya haramta bayar da izinin mika makamai ga wadanda aka san za su yi amfani da makaman wajen aikata laifukkan yaki".

"Har yanzu akwai ayar tambaya a kan halascin bayar da makamai da kasashen Faransa da Birtaniya da Amurka suka yi, kuma ya kamata kotunan cikin gida su bincika", inji kwararrun.

Daya daga cikin kwararrun da suka rubuta rahoton Melissa Parke 'yar kasar Australia, ta shaida wa manema labarai a birnin Geneva cewa:

"A bayyane yake karara cewa ci gaba da samar da makamai ga bangarorin da ke yakar juna a rikikcin na ci gaba da tsawaita rikicin da kuma irin wahalhalun da jama'ar Yemen ke sha".

Masanan sun kuma tattara jerin sunayen wasu mutane masu alaka da aikata manyan laifuka a fadin duniya a inda hakan ta samu sannan suka mika wa hukumar kare hakkin dan Adam ta duniya sunayen a sirrance.

Rundunar hadin gwiwar da Saudiyya ke jagoranta da gwamnatin Yemen da 'yan tawayen Houthi ba su ce komai a kan rahoton ba.

Amma a baya dukkansu sun sha musanta aikata laifukan yaki.

Wani mai magana da yawun gwamnatin Birtaniya ya ce: "Birtaniya na kan gaba a kokarin da kasashen duniya ke yi na ganin an samu mafitar diflomasiyya a rikicin na Yemen mai ban takaici.

"Gwamnatinmu na daga cikin kasashe masu ingantattun tsarin cinikayya da kasashen ketare a fadin duniya."

A baya, ministocin Birtaniya sun ce ba za su iya cewa bamabamai ko jiragen Birtaniya ne suka yi sanadiyyar mutuwar fararen hula a Yemen ba, kasacewar rundunar hadin gwiwar ba ta bin diddigin yadda ake amfani da su.

Amurka na adawa da dakatar da sayarwa ko bada gudumawar makamai a rikicin Yemen din, inda ta ce cigaba da samar da makaman na iya rage yawan rayukan fararen hular da za su iya salwanta a rikicin.