MDD: Al'ummar Yemen na fama da Fari

An wallafa

Shugaban hukumar ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce kungiyoyin agaji na kasashen waje ba sa samun nasara a kokarin da suke na yakar Fari a kasar Yemen.

Ya ce lamarin ya kazanta a makwannin da suka gabata, saboda mutane ba su da abincin da za su ci ya yin da kananan yara ke fama da rashin abinci mai gina jiki.

Mark Lowcock ya ce mutane miliyan 3.5 ne za su karu kan sama da miliyan takwas da ke fama da matsananciyar yunwa a kasar Yemen.

Daman tuni mummunan Fari ya samu wurin zama a kasar, ciki har da rahotannin mutane na cin ganyayyaki saboda ba su da wani abu da za su ci don rayuwa.

Lowcock ya ce yawancin 'yan kasar ba su da hanyar samun kudaden shiga, ciki har da malaman makaranta da yaki ya daidaita makarantun da suke koyarwa da jami'an lafiya wadanda hare-hare ta sama da kasa suka yi wa kashi 60 cikin 100 na sibitocin illa wasu ma sun zama kufai.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kawancen da Saudiyya ke jagoranta a yakin da ake yi da 'yan tawaye mabiya darikar shi'a na kabilar Houthi ke ci gaba da luguden wuta akansu, musamman garin Hudaida da ke gabar teku.

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa matuka, saboda ta nan ne kayan agajin da kasashen duniya ke kai wa 'yan Yemen ya ke isa kasar.