Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gasar Hikayata ta canza rayuwata – Gwarzuwar gasar
Gwarzuwar Gasar Rubutun Kagaggun Labarai ta Hikayata ta 2017 Maimuna Idris Beli ta ce nasarar da ta samu ta sauya bangarori da dama na rayuwarta.
Sashen Hausa na BBC ya kirkiri gasar rubutu ta Hikayata ne domin bai wa mata zalla damar damawa da su a harkar rubutun adabin Hausa kuma ana gudanar da ita ne duk shekara.
Alkalan gasar kan zabi mutum uku wadanda labaransu suka zarce saura domin ba su kyautuka, wadanda kuma a cikinsu ne za a zabi gwarzuwa. A'isha Sabitu ce gwarzuwar gasar ta 2016.
Maimuna Idris ta yi nasarar zama gwarzuwa ne a 2017 da labarinta mai suna "Bai Kai Zuci Ba".
"Shekara biyun da na yi bayan lashe wannan gasar sun rinjayi shekara 15 da na yi ina rubuce-rubuce ta fuskar tasiri a rayuwata. Ta dalilin wannan gasa an kara sanina sosai a duniya," in ji Maimuna.
"Sannan kuma na samu sauki wurin neman aiki bayan da na saka nasarar a takardata ta neman aiki (CV). Da zarar an zo kaina sai a ce ai za ta iya."
Za a rufe shiga gasar bana ne ranar 30 ga watan Agusta, wadda aka bude a ranar 15 ga watan Afrilun 2019.