Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Na je aikin hajji ta dalilin Gasar Hikayata – A'isha Sabitu
A'isha Muhammad Sabitu, wadda ita ce gwarzuwar gasar Hikayata ta 2016, ta ce ta samu alkairai iri-iri bayan da ta zo ta daya a karon farko da aka kaddamar da gasar a 2016.
A'isha ta ce ta sanadiyyar nasarar lashe gasar aka dauke ta aiki sannan kuma ta je aikin hajji.
"Akwai wuraren da a da mutum bai isa ya shiga ba amma ta dalilin gasar yanzu ana karrama ni," in ji A'isha.
Sashen Hausa na BBC ya kirkiri gasar rubutu ta Hikayata ne domin bai wa mata zalla damar damawa da su a harkar rubutun adabin Hausa kuma ana gudanar da ita ne duk shekara.
Za a rufe shiga gasar ta bana ranar 30 ga watan Agusta, wadda aka bude a ranar 15 ga watan Afrilun 2019.