Zidane ya sauya shawara a kan Gareth Bale

Gareth Bale da Tony Kroos

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bale ya ci wa Real Madrid bal 102 tun lokacin da ta sayo shi daga Tottenham a watan Satumba na 2013
An wallafa

Zinedine Zidane ya ce Gareth Bale zai ci gaba da zama a Real Madrid bayan da dan wasan na Wales ya taimaka Karim Benzema ya ci wa kungiyar bal din farko a karawar da ta doke Celta Vigo 3-1.

An yi mamakin yadda kociyan ya sa Bale a wasan tun daga farko, bayan maganar da ake cewa zai bar kungiyar a bazarar na.

Amma kuma sai ga shi ya kasance cikin a wasan da Real din ta ji dadinsa sosai, har ma kociyan yana cewa daman Bale din yana cikin tsarinsa a wasan na Asabar.

Kociyan ya ce, ''Zai ci gaba da zama a nan, saboda haka dukkanninmu ya kamata mu dauki hakan a matsayin wani abin alheri,''

Ya kara da cewa: ''Raunin da Eden Hazard ya ji illa ne a wurinmu, amma hakan bai sauya shirin da muka yi wa Bale ba a wasan.''

Tun da farko Bale ya kai wani wawan hari, kafin daga bisani ya ba wa Benzema bal din da ci wa Real Madrid ta farko a minti na 12.

Celta sun yi tsammani sun rama a daidai lokacin tafiya hutun rabin lokaci, amma na'urar bidiyo mai taimaka wa alkalin wasa ta nuna cewa bal din da Brais Mendez ya ci, ya yi satar gida.

Tony Kroos ya kara ci wa Madrid ta biyu, kafin sannan alkalin wasa ya kori Luka Modric saboda ketar da ya yi wa tsohon dan wasan Arsenal da aka ba da aro Denis Suarez.

Duk da an fitar musu da dan wasa daya, Real sun kara bal ta uku a gidan masu masaukin nasu, Estadio Municipal de Balaidos, ta hannun Lucas Vazquez a minti na 80.

Celta ba su bari a tashi ba tare da sun lasa ko da daya ba, inda dan wasansu da ya shigo a kashi na biyu na fafatawar, Iker Losada ya kwarara wa Thibaut Courtois wata bal, ta kwana a raga, a daidai lokacin tashi.

Wannan nasara ta wasanta na farko ta sa Real Madrid ta kasance ta daya a kan tebur da maki uku, sai bambancin kwallo biyu.

Yayin da babbar abokiyar hamayyarta, Barcelona wadda ta yi rashin nasara a wasanta na farko ranar Juma'a da ci 1-0 a hannun Athletic Bilbao, ta zama ta 18 da bashin bal daya, a teburin mai kungiyoyi 20.

Sakamakon sauran wasannin La Liga na Asabar din nan;

Valencia 1-1 Real Sociedad

Mallorco 2 -1 Eibar

Leganés0- 1 Osasuna

Villarreal 4-4 Granada

Ga sauran wasannin da za a yi na makon na farko na gasar ta La Liga ranar Lahadi 18 ga watan Agusta 2019, da kuma lokacinsu;

Deportivo Alavés16 : 00 Levante

Espanyol 18 : 00 Sevilla

Real Betis 20 : 00 Real Valladolid

Atlético Madrid 21 : 00 Getafe