Hajj 2019: Alhazan Najeriya 45,000 sun fara aikin hajji

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar da ke kula da harkokin aikin hajji a Najeriya (NAHCON) ta bayyana cewa a bana Musulmin kasar 45,000 ne suke aikin hajjin bana a kasar Saudiyya.
Hukumar ta bayyana cewa maniyyatan kasar shida ne suka rasu gabanin fara aikin hajjin.
Kwamishinan Gudanarwa na hukumar Abdullahi Modibbo Saleh ya shaida wa BBC cewa duka maniyyatan da suka mutu "lokacin su ne ya yi."
Har ila yau ya ce kimanin mutum 45,000 ne suka isa kasar don gudanar da aikin Hajjin bana wadda ake sa ran akalla mutum miliyan biyu daga sassan duniya daban-daban za su gudanar da ibadar, wanda shi ne taron jama'a mafi girma a duniya.
Ya kuma ce akwai kimanin maniyyata 300 daga jihar Kano da ba za su samu damar yin aikin ibadar ba saboda matsalolin sufuri.
A ranar Asabar, 9 ga watan Dhul Hijjah, 1440 BH ne za a yi hawan Arfa, mafi muhimmanci a aikin Hajji.
Aikin hajji dai na daya daga cikin shika-shikan addinin Musulunci biyar, da kowace shekara miliyoyin Musulmi daga sassa daban-daban kan hallara a kasar Saudiyya domin aiwatarwa.







