Bama-bamai sun kashe mutum 14 a Kabul

Asalin hoton, Reuters
Akalla mutum 14 ne suka mutu sannan kimanin 150 sun samu raunuka sakamakon tashin bam da ke mota wanda aka nufi wani ofishin 'yan sanda da ke Kabul, babban birnin Afghanistan.
Kungiyar Taliban ta yi ikrarin kai harin wanda yake zuwa ana tsaka da tattaunawa tsakanin Amurka da 'yan kungiyar.
Dukkanin bangarorin biyu dai sun ce ana samun ci gaba a tattaunawar wadda ake yi da manufar kawo karshen rikicin da ya kwashe kusan shekaru 18 ana fama da shi.
Kungiyar Taliban ta ce ta hari 'cibiyar daukar jami'an tsaro' inda ta ce ta samu nasarar kashe 'yan sanda da sojoji da dama.
Ko yaushe Afghanistan za ta yi lafiya?
Da alama har yanzu akwai sauran rina a kaba dangane da warware rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a tsawon shekaru wanda ya jefa kasar ta Afghanistan cikin halin ni-'ya-su
Sai dai masu sharhi na ganin akwai yiwuwar ganin haske sakamakon fara zaman tattaunawa tsakanin Amurka da kungiyar Taliban da aka yi a karshen mako
Wakilin Amurka na musamman, Zalmay Khalilzad ya fadi cewa an samu "ci gaba sosai" a yayin zaman tattaunawar da aka yi a karshen mako a Qatar kuma yana fatan za a ci gaba da tattaunawar.
Wasu daga cikin yarjejeniyoyin sun hada da dauke sojojin Amurka daga Afghanistan bisa sharadin Taliban ba za ta yi amfani da masu tsananin kishin addini ba wajen kai wa muradan Amurka hare-hare ba
Taliban za kuma ta fara tattauna wa da tawagar gwamnatin Afghanistan bisa sharadin cewa za a tsagaita wuta.
'Yan Taliban sun dade suna zillewa daga zaman tattaunawa da gwamnatin Afghanistan har zuwa a amince da jadawalin ficewar sojojin Amurka.
A yanzu haka dai kungiyar Taliban na iko da yankunan kasar fiye da wadanda ta mulka a lokacin da take mulkin kasar kafin kifar da ita a 2001.
Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna yadda gwamnatin Afghanista da sojojin Amurka suka kashe fararan hula 717 a farkon 2019 fiye da 531 da 'yan Taliban.














