Dan sama-jannatin Afirka ya mutu

Asalin hoton, AFP/GETTY IMAGES
Mutumin wanda ake masa da lakabi dan sama-jannatin Afirka da ya mutu a hadarin irin babban babur din nan, da zai kasance bakar fata na farko daga nahiyar da ya je sararin samaniya.
Mandla Maseko mai shekara 30, na bayyana kansa a matsayin cikakken misali na dan talaka, daga birnin Pretoria, wanda aka horar da shi kan yadda zai iya tunkarar duk wani kalubale na rayuwa, gaba-gadi, ba tare da wani shakku ba.
Mandla wanda yake harkar sanya kade-kade da wake-wake lokaci zuwa lokaci, wanda kuma sojan sama ne na Afirka ta Kudu, ya shafe mako daya yana samun horon da ya ce mai tsanani a tashar 'yan sama jannati ta Amurka, da ke Florida, wato Kennedy Space Centre.
A shekara ta 2013, sojan saman na Afirka ta Kudu ya yi nasara a kan mutane miliyan daya ya kasance daya daga cikin mutane 23 a makarantar harkokin sararin samaniyar ta Amurka, da ta shirya ziyarar zuwa samaniya.
Bayan da ya ci gasar da aka yi ta zaben wadanda za a dauka zuwa yawon buda idanu a sararin samaniyar, ya ce yana son ya yi abin da zai karfafa wa matasa a Afirka guiwa, wanda zai tabbatar musu cewa za su iya cimma duk wani buri da suke da shi, ko daga wace irin rayuwa ko gida suka fito.
Sai dai kuma ba a kai ga tashin kumbo ko jirgin sama-jannatin ba, sai ga shi kwatsam, mai faruwa ta faru, mutuwa ta katse masa hanzari.
Mandla Maseko ya yi niyyar kiran BBC ta tarho, idan da ya je sararin samaniyar kamar yadda, Neil Armstrong, mutumin da ya fara sanya kafarsa a duniyar wata ya yi.
Ba-Amurke, Armstrong, wanda shi ne mutum na farko da ya fara tafiya a duniyar wata a shekara ta 1969, ya rasu a 2012 yana da shekara 82 a duniya.
A wata sanarwa da 'yan gidan su Mandla suka fitar sun bayyana cewa mutumin da yawancin 'yan Afirka ta Kudu ke kiransa ko suka san shi a matsayin Spaceboy ko Afronaut wato dan-sama-jannati na Afirka, Mandla Maseko, kwana ya kare, ranar Asabar a wani hadari.
Ya mutu ne a wani hadari na irin katon babur din nan, na kasaita, makamancin wanda dan shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari ya yi hadari da shi a watan Disamba na 2017, a birnin Abuja.











