Birnin Babila ya samu matsayin duniya

Kofar Ishtar

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Samfurin Kofar Ishtar wadda tana daya daga cikin abubuwa bakwai na ban-mamaki a duniya
An wallafa

Hukumar kula da al'adu, ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO, ta zabi birnin nan mai dimbin tarihi na Babylon ko Babila, wanda ke cikin kasar Iraqi, a matsayin daya daga cikin wuraren tarihi na duniya.

Babylon ko Babila na daya daga cikin fitattun manyan birane na tarihi na zamanin da a duniya, inda ya yi fice wajen al'adu da gine-gine da abubuwa na ban mamaki kamar lambuna dake saman gine-gine.

Babban birnin na Sarki Nabonidus, ya kasance ne a tsakanin kogi mafi tsawo a kudu maso yammacin nahiyar Asiyaa, wanda da ya tashi daga Turkiyya ya kwarara zuwa kudu maso gabashi ya ratsa Syria da Iraqi, wanda ya kasance daya daga cikin biyun da ke samar da ruwa ga Kogin Tigris na Iraqin, a yankin da ya kasance asalin inda ci-gaban duniya ya samo asali.

Wani daga cikin ire-iren kayan tarihi na birnin Babylon ko Babila

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto, A shekara goma da ta wuce an yi kokarin gyara abubuwa da dama na tarihi da aka bata na birnin a zamanin Saddam Hussein da kuma lokacin sojin Amurka

Birnin Babila, birni ne da ya yi suna a kan kayatattun lambuna da ake yi a sama ko benaye, maimakon na kasa da aka saba gani a wurare, da kuma kofofi masu ban sha'awa ginin gwanaye - kamar Ishtar Gate, wadda tana daya daga cikin abubuwan ban mamaki 7 na ainahi na duniya.

To sai dai a wannan zamani an bata birnin mai dimbin tarihi inda aka jirkita shi daga ainahin yadda ya samo asali ko aka san shi.

An jirkita shi domin gina wa Saddam Hussein fada, sannan kuma su ma sojojin Amurka suka biyo baya da tasu bannar, a lokacin yakin Iraqi, inda ya kasance sansaninsu, bayan da suka kama shi.

'Yan Iraqi na murnar ba da matsayin

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, 'Yan Iraqi na murnar ba wa birnin na Babila wannan matsayi

Ba wa wuri wannan matsayi na wurin tarihi na hukumar ta kare al'adu ta duniya yana nufin kare shi a matsayin wanda yake da matukar muhimmanci ga dukkanin bil-adama.

An jima ana mamakin yadda wannan birni da ya yi suna wurin abubuwa na ban mamaki nasa bai kasance cikin wuraren na tarihi na hukumar ta duniya ba, tun da farko.