Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wuta kashe masu satar mai daga bututu a Legas
Mutum biyu ne suka mutu sannan motoci guda 30 suka kone kurmus a wutar da tashi sakamakon yoyon bututun man fetir a Ijegun na birnin Legas da safiyar Alhamis.
Hukumar Agajin Gaggagawa ta jihar Legas, LASMA, ta ce mutanen biyu da suka mutu su ne suka haddasa wutar a lokacin da suke kokarin arce wa daga jami'an tsaro bayan an gano suna kokarin satar man daga bututun man da ke yoyo.
Duk da cewa babu cikakken bayani kan ko mutum nawa ne suka jikkata, jami'i a hukumar ta LASMA ya ce suna hada kididdiga.
Tuni dai jami'an Hukumar Kashe Gobara ta jihar Legas suka kashe wutar amma sun gargadi mazauna yakin da su yi nesa da wutar.
Ga abun da wasu ke fadi kan tashin wutar:
Wannan yana cewa ne jami'in kashe gobara daya ne kawai a nan.......Ijegun na ci da wuta
Karin bayani
Wakilinmu a Legas Umar Shehu Elleman ya ce wutar ta gawurta wacce ta tsoratar da jami'an kashe gobara da kuma mazauna yankin bisa la'akari ta shafe sa'oi kafin a dan shawo kanta.
Duk da jami'an sun ci karfin wutar inda suka yi ta amfani da maganin kashe wuta da ke a cikin wasu manyan randuna amma dai jami'an kashe gobara na da shakkun in wutar ta gama mutuwa.
Ko da ya ke babu cikakkun alkaluman wadanda su ka mutu ko kuma aka raunata ba to amma kamar yadda babban jami'in hulda da jama'a na hukumar kai agajin gaggawa ta kasa, Ibrahim Farintoye yace a yanzu suna da wasu alkaluma da za a iya cewa sune adadi na baya.
Ya ce "kawo wannan lokaci ba mu san adadin man fetur da ya rage a cikin tankar ba."
Daga kididdigarmu motoci kimanin 30 da daya ne suka kone, ba mu sani ba ko akwai sauran wasu.
Tuni aka garzaya da mutum 12 da wutar ta kona su. Abin da jami'an hukumar kashe gobara suke yi shi ne su tabbatar da wutar ba ta watsu zuwa wasu sassa ba.
Ya kara da cewa musabbabin afkuwar lamarin ya dauko asali bayan da mazauna wannan unguwa suka fadawa jami'an tsaro cewa wasu na kwasar ganimar man fetur a unguwar ta Ijegun.
To a lokacin da jami'an tsaro su ka zo domin dakatar da kama su, shine matasan suka cinnawa babbar motar wuta.
Bincike ya nuna manyan motoci hudu ne makare da ma fetur bayan masu fasa bututun man fetur a yankin suka yi. To amma uku daga cikin su, suka tsallake a yayin da babbar tanka daya ta kama da wuta.
Bincike ya nuna gobarar da babbar motar mai dauke da man fetur ta haddasa a wajen Legas dai ba shine na farko ba, bisa la'aari da aka samu manyan motocin na faduwa kuma su kama da wuta.
Ko a watannin baya wata babbar mota dauke da man fetur ta fadi a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan da ta hallaka mutane da kuma kona motoci sama da 30 kurmus.
Za dai ace wannan ba shine karshen ceto da ake yi ba, domin kuwa a cewar wata babbar jami'ar kashe gobara za su tabbatar da an kawo karshen wannan gobara bisa la'akari da yadda harshenta ya tsallake zuwa wasu sassa.
Gobarar kamar yadda shaidun gani da ido suka nuna ta faru tun da jijjifin safiyar ranar Alhamis.
Hukumomi da abin ya shafa sun ce za su samu nasarar kawo karshen ta. Kamar dai yadda wata babbar jami'a a hukumar kashe gobara ta jihar Legas ta nuna.
Wutar ta baya baya dai ta zo kwanaki uku bayan wata babbar tanka dauke da man fetur ta yi sanadin mutane da dama a jihar Benue, a yayin da suke kwasar ganimar ma fetur daga motar da ta sa mu matsala.
Mutane da yawa dai na fargabar wanann wuta za ta fadada zuwa gidajensu. To amma Mr. Femi Osanyitolu, babban manajan darakta a hukumar kai agajin gaggawa ya ce jama'a su kwantar da hankulansu.
Ya ce: "ceto da kiyaye rayuka da dukiyar al'umma na a gaba gaba da wanann gwamnati ta jihar Legas ke ba shi muhinmanci.
"Mu na kira ga al'ummar jihar Legas da su kwantar da hankalinsu, muna tabbatar mu su cewa mun killace wannan wuta kuma ba za ta kai ga gidajensu ba."
Ijegun a inda wutar ta kama bayan farmakin da aka kaiwa tankar mai dauke da man dai ta kasance unguwar marasa galihu da ke a wajen birnin Legas kuma tsukakken yanki ne da mafi yawa inda'yan Rabbana ka wadata mu su ka yi kaka-gida.
An ruwaito cewa matasa masu zaman banza na anfani da kusancin bututun man fetur suna aikata ta'asar kwasar gani ba dare ba rana.