'Mara lafiya helikofta ya dauka a Legas'

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Mutumin da jirgi mai saukar ungulu ya dauka daga cikin cunkoson ababan hawa a birnin Legas na Najeriya na fama da cutar bugun jini, kamar yadda kamfanin helikoftan ya shaida wa BBC.

A ranar Lahadi ne dai wani bidiyo ya bazu a kafafen sada zumunta inda aka ga jirgi mai saukar ungulu ya dauki mutumin a tsakiyar cunkoson ababan hawa, al'amarin da ya sa wasu tinanin cewa mutumin hamshakin mai kudi ne.

Wannan bidiyo dai ya janyo suka daga 'yan Najeriya kan irin halayyar masu dukiya a kasar.

To sai dai kamfanin jirgin ya ce ba wani abu ba ne wanda ba a saba gani ba kasancewar kamfani ya saba kai wa marasa lafiya dauki.

Kamfanin ya ce mutumin ya yi fama da hawan jini, abin da ya sa direbansa ya shiga dimuwa.

Femi Adeniji wanda ya yi magana da BBC, ya ce jirgin kamfanin nasu ya dauki marar lafiyar tare da likitansa,

Bidiyon ya bazu a shafin sadarwa na Instagram. Latsa nan domin kallon abin da ya faru

Da alama mai wannan shafin na Instagram da ke amfani da suna Julian's Luxury ne ya fara baza wannan bidiyo.

Ya ce "Rayuwar kasaita... Karfin dukiya... daukar mutum mai matsayi wanda ya makale a cunkoson ababan hawa a kan titin Legas zuwa Benin."

An kuma ta yada jita-jitan cewa jirgin ya je daukar wata budurwar wani hanshakin mai kudi ne.

Kwana uku bayan nan sai Hukumar da ke kula da Sufurin Jiragen kasar, ta ce ta fara bincike a kan al'amarin.