Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hotunan da ba a taba gani ba na harin 9/11 na Amurka
Masu adana faye-fayen CD a wani wajen ajiya ya gano hotuna na Cibiyar Kasuwanci Ta Duniya da ke New York bayan harin da aka kai Amurka na 9/11 a shekarar 2001.
Hotunan sun nuna kamar wani ma'aikaci daga cikin masu aikin gini ne ya dauke su wanda ya taimaka aka kwashe baraguzan Cibiyar Kasuwanci Ta Duniya da kewaye.
Faye-fayen CD din sun lalace amma an samu damar kwashe bayanan da suke ciki.
Masu adana faye-fayen CDn sun saka hotunan a shafin Flickr.
Kundin hotunan na intanet sun hada da na Cibiyar Kasuwanci Ta Duniya na kasanta da can sama, da masu aikin gini da kuma yadda cikin ginin ya lalace.
Kusan mutum 3,000 ne suka mutu a yayin da aka karkatar da akalar jirage hudu zuwa Cibiyar Kasuwanci Ta Duniya a New York da ginin Pentagon da kuma wani waje a Pennsylvania.
"Wadannan abubuwa an banzatar da su ne a wajen baje koli. Da ba mu je wajen ba da yanzu wadannan hotuna na cikin shara," in ji Dr Jonathan Burgess, wanda abokiyar zamansa ta gano hotunan a wajen baje koli.
Daga nan sai Dr Burgess ya adana hotunan ya kuma fitar da su ta hanyar wani abokin aikinsa Jason Scott.
"Abin al'ajabi ne yadda aka fitar da hotunan daga faya-fayen CDn duk da tsufansu."
Ya yi amfani da wata manhaja ne ya fitar da hotunan.
Dr Burgess ya ce shi da Mista Scott har yanzu ba su samu nasarar gano wanda ya dauki hotunan ba ko wani dan uwansa.
Da yawan wadanda suka yi aiki jim kadan bayan faruwar harin na 9/11 sun yi ta fama da rashin lafiya, inda kuma aka yi amannar cewa kusan mutum 400,000 ne abubuwan da ke da guba suka shafe su, ko suka jikkata ko suka dimauce a ranar da abin ya faru, a cewar Cibiyar Kare Yaduwar Cututtuka ta CDC.
Dr Burgess ya ce yada hotunan "yin abin da ya dace ne ga bil'adama."
Ga dai wasu hotunan da aka dora a shafin Flickr.
.