Kalli hotunan yadda zafi ya addabi nahiyar Turai

Wasu ma'aurata na sunbatar juna a gaban hasumiyar Eiffel

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Zafi ya sanya 'yan yawon bude ido da jama'ar gari fita zuwa gaban hasumiyar Eiffel ranar Talata a birnin Paris na Faransa
An wallafa

Mutane da dama a fadin nahiyar Turai na kokarin kaucewa tsananin zafi da ake fama da shi a lokacin da yanayi ke kara hauhawa.

Yanayin wanda masana suka ce ka iya yin kisa - ya tsananta ne saboda iska mai zafi da ke fitowa daga yankin Sahara - kuma tuni ya sa aka soke jarabawar 'yan makaranta a Faransa.

Sai dai masanan na hasashen yanayin zafin a kasashen Faransa da Jamus da Belgium zai iya kai wa matsayin da ba a taba gani ba a 'yan kwanaki masu zuwa.

Masu yawon bude ido dauke da lema

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mutane na amfani da lema dan kare rana a birnin Roma
Wani mutum na tafiya, ya yin da wasu mata ke daukar hoton dauki da kanka

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Can a birnin Nice na Faransa, tsananin zafi ya kai maki 33 a ma'aunin selshiyos a ranar Litinin
Yara na shiga tafkin Geneva

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Yara sun yi amfani da wannan damar don shiga tafkin Geneva a kasar Switzerland
Matasa na fadawa ruwa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Zafin da ake yi ya sanya matasa na kundunbala a Birnin Copenhagen, da ke Denmark
Yara na wasa a ruwa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wannan hoton wani yaro ne da ya ke wasa a wani karamin kududdufi marar tafiya a birnin Reins a kasar Faransa
Yara ne ke kasan wani tsauni da ke zubo da ruwa

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Birnin Madrid na Sifaniya kuwa, dole yara suka tsaya kasan wani tsauni da ke zubo da ruwa saboda zafi
Dabbobi ma su na jin tsananin zafin

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani ma'aikacin gidan namun daji ke Birnin Berlin na kasar Jamus ke fesawa wata Giwa ruwa da mesa dan rage mata zafin da ta ke ji
Mutane na tuka kwale-kwale

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu mutane ke tuka kananan jiragen ruwa a tekun Danube na birnin Vienna a kasar Austriya
Wata mace na motsa jiki

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto, Sai dai birnin Landan yanayi mai dadi ake yi inda rana ta dan fito kadan, saboda makwannin da suka wuce an yi ruwa mai hade da iska. Amma duk da haka wasu na dakon fitowar rana a kwanaki masu zuwa

Duka hotunan na da hakkin mallaka