Falasdinawa sun watsawa Trump kasa a ido

Asalin hoton, AFP
Jagoran Falasdinawa Mahmud Abbas ya yi watsi da sabon shirin da Amurka ta sanar na samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.
Shugaban ya ce ba za su amince da duk wani yunkuri da bai hada da batun sasantawa ta siyasa da Isra'ila ba.
Karkashin yarjejeniyar da Trump da surukinsa, kuma mai ba shi shawara Jared Kushner, suke son samarwa, za a bai wa Falasdinawa sama da dala biliyan 25 domin gudanar da ayyukan ci gaba, tayin da da shugaban Falasdinawa ya yi watsi da shi.
Ya ce za su kauracewa taron tattauna kudirin da za a yi a Manama, babban birnin kasar Bahrain.
"Ba na tunanin akwai wani sakamako mai kyau da za a samu daga taron Manama, saboda tun da farko an gina shi ne kan kuskure, kuma duk abin da aka gina kan karya, to karya za a samar".
Mahmud Abbas ya kara da cewa ba za a tursasawa Falasdinawa su sanya hannu kan wata yarjejeniyar da ba su amince da ita ba.
"Ba za mu zama bayi ko fadawan Kushner da Greenblatt da Friedman ba".
Ba za su amince da Amurka ita kadai ba a matsayin wadda za ta shiga tsakani kan batun Gabas ta Tsakiya ba.
"Akwai kwamiti na kasahsen duniya, su ne masu shiga tsakani amma ba Amurka ba, ba mu yarda da manufofin Amurka ba, kuma ba mu amince da Amurka ita kadai ba," a cewar Mista Abbas.
Kawo yanzu dai Amurka ba ta mayar da martani kan kalaman na jagoran Falasdinawan ba.











