Ahmed Lawan ya 'harzuka' wasu 'yan jam'iyyarsa ta APC

Sanata Ahmed Lawan

Asalin hoton, NAtional Assembly

Bayanan hoto, An dade ana kamfe da kulla-kullar siyasa kan takarar Ahmed Lawan, inda ya kayar da Ali Ndume
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Jama'a da dama a Najeriya na ci gaba da muhawara kan yadda Shugaban Majalisar Dattawan kasar ya kama ragamar kujerar da aka zabe shi akai, inda wasu ke ganin ya fara da kafar hagu, yayin da wasu ke cewa dama sun san za a rina.

A ranar 11 ga watan nan ne aka zabi Sanata Ahmed Lawan wanda ke wakiltar Yobe ta Arewa domin jagorantar majalisar ta tara bayan shafe watanni aka kamfe da kamun kafa, inda ya kayar da Ali Ndume daga jihar Borno.

Sai dai jim kadan bayan zaben na sa, sai ya fara tsintar kansa a rudani, inda da dama daga cikin 'ya'yan jam'iyyarsa ta APC suka yi masa rufdugu kan mutumin da ya nada a matsayin mai magana da yawunsa, suna fargabar ka da "su tura mota ta bude su da kura".

Cikin wadanda suka goyi bayan masu sukar nadin Festus Adedayo har da Uwargidan Shugaban kasa Aisha Buhari, da wasu fitattun magoya bayan gwamnati da APC.

Duka sun zargi Adedayo, wanda gogaggen dan jarida ne da ya shahara wurin sharhi kan al'amura, da cewa ya yi kaurin-suna wurin sukar manufofin gwamnatin Buhari.

Haka kuma masu adawa da nadin nasa sun rinka amfani da maudu'in #SackfestusAdededayo wato a kori Festus Adededayo a shafukan sada zumunta domin matsawa Ahmed Lawan lamba kan ya sauke shi.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

@cbngov_akin1 ya ce ya kamata @DrAhmadLawan ya sani cewa nadin Festus Adedayo abin dariya ne a wurinmu. Ba za ta sabu ba. Kalli wata makala da ya rubuta a bara yana sukar shugabanmu da kuma APC".

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Yain da @KemisolaAdekun1 ta ce "...ta yaya mutumin da ya yi kaurin suna wurin sukar gwamnati kuma zai karbi mukami a cikinta. Wannan ya fito da halinsa a zahiri. Zai iya juyawa mai gidan nasa baya".

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Ana cikin hake ne kwatsam sai Sanata Lawan ya soke nadin na Adedayo, kamar yadda mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Muhammed Isa ya sanar, ba tare da bayyana dalili ba.

Sai dai anasa bangaren, dan jaridar ya wallafa wani sharhi a shafin Premium Times, inda ya ce ba shi "ya nemi mukamin ba tun asali, kuma ba zai taba sauya matsayinsa kan yadda yake kallon al'amuran yau da kullum a Najeriya ba".

Ya ce tun "shekarar 1998 da na fara sharhi a jaridu, kusan babu wani shugaban kasa ko manyan jagororin siyasa da suka tsira daga suka a wurina, a don haka ba ni da jam'iyya ko gwamnati".

Presentational grey line

Ba a nan ta tsaya ba

Sanata Ahmed Lawan

Asalin hoton, Senate

Bayanan hoto, Ahmed Lawan ya shafe shekara 20 a majalisar tarayya

Tun da farko dai Sanata Lawan ya fara ne da kokarin kare kansa bayan da wasu kafafen yada labarai suka lakaba masa wani labari da ke cewa ya nemi jam'iyyar APC da Shugaba Buhari da su mika mulki ga yankin Arewa maso Yamma a shekara ta 2023.

Wannan ta sa sai da ya fito ya karyata labarin, inda ya ce wani takwaransa ne, wato sakataren APC na jihar Adamawa, ya yi maganar ba shi ba.

Wani jigo a jam'iyyar APC wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa BBC cewa ganin irin ja-in-jar da aka yi kan takararsa da yadda ta ja hankalin 'yan kasar, wani zai yi tunanin cewa Ahmed Lawan zai yi taka-tsantsan a duk irin abubuwan da zai yi.

"Amma abin mamaki sai ga shi ya fara wa'adin nasa da haifar da rudani. Muna fatan ba za a sake maimaita irin wannan ba," a cewarsa.

Kawo yanzu dai ba a nada wanda ko wacce za ta maye gurbin Mista Adedayo ba, sai dai da alama 'yan APC za su zura ido domin ganin mutumin da za a nada a karo na biyu.