An yi jana'izar Shugaba Mohammed Morsi bayan ya mutu a kotu

Asalin hoton, EPA
An yi jana'izar Tsohon Shugaban kasar Masar Mohammed Morsi sa'o'i kadan bayan ya mutu a wata kotu inda ya yanke jiki ya fadi a ranar Litinin.
Lauyansa ya shaida wa kamafnin dillancin labarai na AFP cewa an binne shi ne a birnin Alkahira ranar Talata da safe a gaban iyalansa.
Morsi, mai shekara 67, ya kasance a gidan yari tun lokacin da sojoji suka yi masa juyin mulki a shekarar 2013.
Kungiyoyin kare hakkin bil'adama, wadanda suka yi Allah-wadai da halin da aka tsare shi a ciki, sun yi kiran da a gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa kan musabbabin mutuwarsa.
Iyalansa da kuma masu fafutuka sun dade suna kokawa kan tabarbarewar rashin lafiyarsa da kuma lokutan da ake tsare shi shi kadai bayan 'yar ganawar da yake yi da lauyoyinsa da kuma iyalansa.
Dansa, Abdullah Mohammed Morsi, ya gayawa kamafnin dillancin labarai na Reuters cewa mahukuntan Masar sun ki amincewa da bukatar iyalansa na a basu gawarsa domin yi masa jana'iza a bainar jama'a a mahaifarsa.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana shi a matsayin shahidi, sannan ya ce jininsa na kan gwamnatin Masar. Mazauna birnin Istanbul sun yi masa sallar janaza.
Wane ne Morsi?

Asalin hoton, Getty Images
An haifi Morsi ne a kauyen El-Adwah a gabar kogin Nilu a lardin Sharqiya a 1951.
Ya yi karatu a fannin injiniya a Jami'ar birnin Alkahira a shekarun 1970 kafin ya tafi kasar Amurka inda ya kammala digiri na uku a can.
Kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Brotherhood ta tsayar da shi dan takarar shugabancin kasar Masar a shekarar 2012.
Bayan da ya samu nasara a zabe, ya yi alkawarin cewa "gwamnatinsa za ta tafi da duka 'yan Masar".
Sai dai masu suka sun ce gwamnatinsa ta kasa cirewa 'yan kasar kitse a wuta.

Asalin hoton, Reuters
An zarge shi da barin masu tsananin kishin addinin Islama cin karensu ba babbaka a fagen siyasar kasar da rashin iya tafiyar da tattalin arzikin kasar, batun da shi da magoya bayansa suka musanta.
Daga nan ne aka fara samun dimbin masu zanga-zanga adawa da gwamnatin Morsi a titunan kasar lokacin bikin cika shekara daya da hawansa mulki a ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2013.
'Yan kwanaki bayan fara zanga-zangar a ranar 3 ga watan Yuli sojoji suka dakatar da kundin tsarin mulkin kasar, inda suka sanar da kafa wata gwamnatin rikon kwarya kafin gudanar da sabon zabe.
Bayan haka sai sojojin suka kama Morsi, wanda ya yi watsi da matakin hambarar da gwamnatinsa.

Asalin hoton, Anadolu Agency via Getty










