Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kalli shugaban kasa na tikar rawa a bainar jama'a
A ranar Lahadi ne aka yi hutu domin tunawa da ranar Matasa ta Afirka ta Kudu.
Sai dai abin da ya fi jan hankalin mutane a shafukan sada zumunta shi ne wani bidiyo na Cyril Ramaphosa yana tikar rawa a gaban jama'a.
Mutane da dama sun rinka sake wallafa bidiyon a Twitter.
Kawo yanzu sama da mutum 100,000 ne suka kalli bidiyon kuma yawancinsu sun sanya alamun dariya a martanin da suka mayar.
Bikin, wanda ake yi a ranar 16 ga watan Yuni, na tunawa ne da tarzomar da ta faru a shekarar 1976 a birnin Soweto lokacin da dubban dalibai suka yi zanga-zanga domin nuna adawa da mulkin wariyar launin fata da kuma manufofin ilimi.
Daruruwan mutane 'yan sanda suka kashe, lamarin da ya kawo gagarumin sauyi a fannin zamantakewa da kuma siyasar kasar.