Rikicin Sudan: Alkaluman wadanda suka mutu na karuwa

An wallafa

Jami'an tsaron Sudan na kokarin tabbatar da ikonsu a babban birnin kasar Khartoum, bayan hallaka sama da farar hula 100 wadanda ba sa dauke da wani makami, a yayin tarwatsa masu zanga-zangar tabbatar da dumokuradiyya.

Kungiyoyi masu adawa na cewa an samu karin mutanen da aka jefa a cikin wani kogi.

Ana iya ganin dakarun wata kungiyar mayakan sa-kai ta gwamnati wadanda ake jin tsoron su, suna ta sintiri a birnin, inda rahotanni ke cewa suna harbi da duka da kuma kama fararen hula.

Ana ganin a 'yan kawanaki kadan da suka gabata 'yan hamayyar na Sudan ke dab da cimma yarjejeniya da sojojin da ke rikon-kwarya na kasar, kan kafa gwamnatin farar-hula, sai kwatsam al'amura suka tabarbare.

Dakaru masu alaka da gwamnati da ke tarwatsa masu zanga-zangar da suka yi zaman dirshan, sun yi nasarar korar wasu fararen hular, lamarin da ya kai ga sun bar dandalin da suka mamaye, suka ja baya zuwa cikin unguwanni, inda gidajen jama'a suke.

Sai dai kuma masu zanga-zangar sun ci gaba da kakkafa shingaye na datse hanyoyi da duwatsu da kuma tayoyi da suke cinna wa wuta.

Su kuwa dakarun mayakan sa-kai na gwanmnati suna ta sintiri na titunan a birnin a motoci inda suke kokarin kawar da shingayen, suna harbi da dukan masu zanga-zangar da kulake ko sanduna kamar yadda rahotanni suka ce.

Halin da ake ciki a yanzu

Jami'an tsaro sun kai wani samame kan masu zanga-zanga da sanyin safiyar Litinin, inji masu fafutukar suka kafa mulkin demokradiyya.

Kakakin majalisar sojoji da ke mulkin kasar, Laftana Janar Shams al-Din Kabbashi ya ce jami'an tsaron sun kai samame zuwa wani wuri da "aka dade ana ruruta wutar rikicin".

Sai dai wani dan jarida mai aiki a birnin Khartoum ya shaida wa BBC cewa " na kirga gawawwakin masu zanga-zanga guda 11 sannan na ga gawawwakin sojoji guda 16."

Ya kuma kara da cewa "sojoji da farar hula na kai wa juna farmaki."

Yadda rikicin ya samo asali

  • 19 ga Disamba 2018 - rikici ya barke bayan karin kudin man fetur da biredi da gwamnati ta yi
  • 22 ga fabrairu 2019 - Shugaba al Bashir ya rusa gwamnatinsa
  • 24 ga Fabrairu - Zanga-zanga ta ci gaba, jami'an tsaro sun rika harbi da bindiga
  • 6 ga Afrilu - Masu zanga-zanga sun fara zaman dirshan a shalkwatar sojojin kasar
  • 11 ga Afrilu - Manyan hafsoshin sojojin kasar sun bayyana hambare al Bashir daga mukaminsa
  • 20 ga Afrilu - An fara tattaunawa tsakanin gwamnatin sojoji da masu fafutuka
  • 13 ga Mayu - Harbe-harbe a gaban shalkwatar sojojin kasar ya yi sanadin mutuwar mutum shida
  • 14 ga Mayu - Wakilan gwamnatin soja da na fararen hula sun cimma yarjejeniyar mika mulki na shekara uku masu zuwa
  • 16 ga Mayu - An dkatar da tataunawa bayan da gwamnatin soja ta nemi a kawar da asu shingaye a Khartoum
  • 3 ga Yuni - Masu fafutuka sun sanar da jingine tattaunawar da suke yi da majalisar sojojin kasar, kuma sun tuhume su da amfani da karfin soji domin tarwatsa su