Najeriya da Nijar sun amince da kafa matatar mai

Asalin hoton, twitter/IbeKachikwu
Gwamnatin Najeriya da takwararta ta Nijar sun cimma yarjejeniyar gina matatar man fetur a kan iyakar kasashen ta bangaren jihar Katsina, tare da shimfida bututu da zai taso daga cikin Nijar zuwa sabuwar matatar.
Nan da 'yan kwanaki masu zuwa ne kasashen za su sanya hannu a kan yarjejeniyar kamar yadda wata sanarwa da ta fito daga ofishin karamin ministan man fetur na Najeriya Dr. Emmanuel Ibe Kachikwu ta bayyana.
A ranar Laraba ne Ministan na Najeriya ya jagoranci tawagar ma'aikatarsa da ta kamfanin mai na kasar ta gana da Shugaban Jamhuriyar Nijar, Mahamadou Issoufou da Ministan makamashi na Nijar din Foumakoye Gado, a Nijar, inda suka cimma yarjejeniyar.
Sanarwar ta kara da cewa matakin na daga cikin kokarin hadin guiwa da ake yi na tabbatar da wadatar man fetur da dangoginsa a Najeriya.






