Wanne hali raunin Salah zai jefa Liverpool?

Mohamed Salah injured

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mohamed Salah shi ne babban dan wasan da ya fi zura kwallaye a Gasar Firimiya ta bana da kwallo 22
An wallafa

An dauke babban mai zura kwallaye a Gasar Firimiyar Ingila Mohamed Salah a kan gadon marasa lafiya a wasan da kungiyarsa Liverpool ta casa Newcastle da ci 3-2.

An bar dan wasan da rungume kai bayan sun ci kasuwar sama shi da golan Newcastle Martin Dubravka.

Divock Origi ne ya canji Mohamed Salah, wanda ya ci wa kungiyarsa kwallo ta biyu, bayan minti 73 wasa ya yi zafi ana kunnen doki 2-2.

Nan da nan Origi ya nuna kansa a wasan, inda ya ci wa kungiyarsa kwallon da ta ba ta nasara a kan Newcastle, saura minti hudu a busa tashi.

Sakamakon ya nuna cewa sai a wasannin karshe na kakar Firimiyar bana za a iya sanin gwanin da zai lashe gasar wato ranar Lahadi 12 ga watan Mayu.

Da wannan nasara a yanzu Liverpool na saman tebur da ratar maki biyu a kan babbar abokiyar hamayyarta Manchester City, wadda za ta kara da Leicester a ranar Litinin.

Kafin nan, Liverpool za ta fuskanci Barcelona a zagaye na biyu na karawar kusa da karshe a gasar cin kofin Zakarun Turai ranar Talata, don haka raunin da Mohamed Salah ya ji zai kasance wani abin damuwa ga koci Jurgen Klopp saboda kungiyarsa za ta yi kokarin rama kwallo uku da nema da aka zazzaga mata a karawar farko.

Klopp ya fada wa BBC cewa "An buge Mo (Salah) a karon da suka yi da gola, kuma ina jin kansa ya bugu, a zahiri dai mun gan shi garau amma dai za mu ga abin da hali zai yi."