Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Queen Elizabeth II: Rayuwar Gimbiya a filin daga
A nazarin mafi yawan harkokin rayuwarta, Yakin Duniya na Biyu shi ya bude mata babin rayuwa da ya haskata na kasancewarta Sarauniya Elizabeth II
Tana da shekara 13, inda shekaru shida da aka shafe na rikicin yaki suka share mata fagen hada-hadar harkokin rayuwa, inda ta fara fita bainar jama'a a matsayin sarauniyar da za ta gaji sarautar mulki.
Zuri'ar gidan sarauta - Sarki da Sarauniya da 'ya'yansu biyu Elizabeth da Margret su ne tambarin alamar sarautar Birtaniya, wadanda a dalilinsu ne Birtaniya da abokan hadin gwiwarta ke yakar Jamus karkashin jagorancin Adolf Hitler.
An cimma dimbin nasarori saboda a gaskiyar lamari Adolf Hitler ba shi da hakikanin iyali na kashin kansa.
A Oktobar 1940, lokacin da Birtaniya ta yi fama da luguden bama-bamai mafi muni, Elizabeth ta fara yi wa al'ummar kasar jawabi ta kafar yada labarai.
An dai tsara jawabin ne a matsayin sako ga kananan yara, wadanda aka kai su Arewacin Amurka don samun mafakar tsira daga illar luguden bama-baman da aka rika jefa wa biranen Birtaniya.
Kuma an tsara hakan ne don zaburarwa da daukar hankalin Amurkawa su goyi bayan shigar Amurka yakin.
"Mu yaran da ke zaune a gida muna cike da karsashi da kwarin gwiwa," in ji ta.
"Muna iya kokarin ganin mun yi abin da za mu iya yi don taimaka wa jaruman sojojinmu na ruwa da na sama. Sannan mun shirya tarairayar hadari da takaicin bakin cikin da ke tattare da yaki."
Hakikanin gaskiya kasancewar Elizabeth da Margaret a cikin kasar lamarin ya yi matukar bayar da karsashin kwarin gwiwa.
Bam
An bayar da shawarar ganin iyalan gidan sarauta su nemi mafaka a kasar wajen, musamman Kanada, amma Sarki da Sarauniya suka nuna ko-in-kula
"Yaran ba za su fice daga kasar ba in ban fice ba," yadda Sarauniya Elizabeth ta yi ikirari.
"Ba zan fice ba sai dai in iyayensu ne suka yi hakan, kuma Sarki bai zai fice daga kasar ba a kowane irin hali ta kasance." Wuri mafi nisa da aka kai yaran shi ne gidan sarautar Windsor.
"Mun je hutun karshen mako, sai muka zauna har tsawon shekara biyar," in ji su.
Suna da matukar kusanci da inda za su rika hango tartsatsin wuta a sararin samaniyar Landan lokacin da ake ruwan bama-bamai. Akwai lokacin da bam ya fado daf da gidan sarauta.
"Daukacinmu mun kasance cikin damuwa lokacin da muka ji karar," kamar yadda Gimbiya Margaret ta tuna, lokacin da suke zaune a mafakarsu ake kawo hari ta sama.
Wadannan 'yan uwa a mafi yawan yammaci da kwanakin karshen mako iyayensu kan kasance tare da su, sannan an ci gaba da koyar da su karatu, tare da malaman da ke koya musu darussa.
A lokacin Kirsimeti don su bai wa mahaifinsu kwarin gwiwa - wanda ya dugunzuma cikin damuwa bisa la'akari da dimbin asarar rayukan mutanen kasarsa maza da mata - sai wadannan 'yan mata suka gudanar da wasannin kwaikwayon nuni cikin nishadi (babu furucin kalamai sai nunin abin da ake nufi).
Tashin hankali
A Kadaicin shekara guda, Aladdin tare da Gimbiya kusan kodayaushe ya kan zama gwarzon tauraro.
A shekarar 1942 gimbiya Elizabeth ta fara gudanar da harkokin mulki a bainar jama'a, inda ta duba faretin ban girma na rundunar 'yan gadin Grenadier (masu gadin kula da tsaron Sarki da Sarauniya), inda ta samu karramawar mai matsayin Kanar.
Mafi kimar mukamin gudanar da aiki da ta samu ya fito karara cikin al'amuran da suka faru a wadannan shekarun.
A shekarar 1944, inda kacokam Sarki ya kasance cikin bacin rai game da asaratr da aka yi a yakin Arnhem, Elizabeth 'yar shekara 18 da Margaret 'yar shekara 14 dsuka rubuta wasan kwaikwayon nuni cikin nishadi mai taken Kananan jajaye mahaya kofatai - 'Little Red Riding Boots- tare da taimakon mahaifiyarsu.
Masu gadin gidan sarautar da ke bakin aiki, su uku an dan tsarma fitowarsu a wasan. Daya daga cikinsu, Bill Davies, ya tuna yadda aka auna shi, don dinka masa kayan sarki masu walwalin hasken jajaye da fatar yanyawa.
"Wasan ya yi matukar kayatarwa, har ta kai ga iyalan (gidan sarautar) sun tattara hankalinsu wuri guda," kamar yadda ya iya tunawa. "Hikaya ce ta wucin-gadi (wani dan takin lokaci). Mun manta da yaki na tsawon sa'a guda ko biyu."
Farin ciki da annashuwa
A shekarar karshe ta zamanin yaki, Elizabeth ta fito cikin kayan damarar baraden yi wa iyakar kasa hidima, wadanda ake yi wa lakabin ATS.
An yi mata rajistar shiga rundunar da lambar 230873, da lakabin sunan Second Subaltern Elizabeth Windsor, kuma ta shafe makonni uku tare da da wata tawagar rundunar da aka yi matukar lura da su, inda ta koyi kanikancin gyaran mota da tukin babbar mota.
An ce dai lamarin shi ne karo na farko da aka taba samun mace 'yar gidan sarauta ta halarci kwas din koyon aiki tare da "sauran gama-garin mutane."
Kuma shekarun da suka biyo bayan yakin a cikinsu ne ta tsunduma a cikin soyayya tare da Laftanar Philip Mountbatten, daga bisani ya zama mai sarautar gargajiya na magajin garin Duke na Edingburgh, bayan da ya zama mijinta, har ya kasance mai matukar tasiri a harkokin mulkinta.
A Mayun 1945, dubban mutane sun taru a fadar Buckingham don murnar bikin zagayowar ranar samun nasarar Turai.
Winston Churchill ya kasance tare da iyalan gidan sarautar a wannan farfajiyar, inda gimbiyoyi biyu suka fice daga wurin suka shiga cikin taron mutane.
Bayan shekara 40, Sarauniya duk ta tuna wadannan al'amura da suka faru.
"Na tuna jerin gwanon mutanen da ban sani ba dauke da makamai, suna tafiya zuwa titin hanyar zuwa gidan sarauta mai lakabin 'Whitehall.' Daukacinmu kawai mun kasance cikin farin ciki da annashuwa."
"Bayan da muka keta wurin shakatawa na Green Park, sai muka tsaya a waje muna ta kwalla kara, "Muna son Sarki." Ina jin cewa wannan shi ne al'amari mafi muhimmaci a wannan dare da ba zan manta da shi a rayuwata ba."
©Hakkin mallakar hotunan abun kiyayewa ne