Kaunar da Sarauniya Elizabeth take yi wa dawakai

Asalin hoton, Getty Images
Sarauniya ta yi gadon son tseren sukuwar dawakai daga iyayenta, wadanda daukacinsu jajirtattun masu sukuwar dawaki ne.
Duk da cewa mahaifiyarta jigo ce a hada-hadar sukuwar dawaki ta kasa, amma daukacin Gimbiya da mahaifinta sun fi sha'awar sukuwar dawaki.
Elizabeth ta samu kwarin gwiwar hawan doki tun tana karama, kamar yadda ta taba furtawa cewa tana da burin zama hamshakiyar mace mai daraja a kasar da ta mallaki dimbin karnuka da dawakai.
Sha'awarta ga tseren dawaki lamarin ya bijiro ne a zamanin yakin Duniya na biyu, lokacin da ta raka mahaifinta ganin yadda ake horar da dawakan gidan sarauta a Whiltshire.

Asalin hoton, Getty Images
"Na taba su da sha'awarsu, har ta kai ga daga bisani na damfaru da kaunarsu," kamar yadda ta tuna daga bisani. "Ban taba jin santsin walwalin taushin dawakan Birtaniya a da farko ba."
Ta rika kai ziyara a boye garin Newmarket don ganin yadda dawakan mahaifinta ke sukuwa.
Elizabeth ba ta fara tseren sukuwar dawaki a bainar jama'a ba, har sai da aka kammala yaki a Turai, wato cikin Mayun 1945, lokacin da ta raka Sarki da Sarauniya Ascot.
Kusan ko da yaushe taron na samun tagomashin sarauta (halartar Sarki da Sarauniya), kuma bayan darewartar karagar mulki a shekarar 1952, sai ta zabura wajen ci gaba da gudanar da wannan al'ada, a matsayin daya daga mafi soyuwar tarukan haduwarta da jama'a.
Launuka
Ta samu nasara zagayowar karo na biyu a matsayinta na wadda ke mallaka da kiwon dawaki. Kakkarfan dokin Aureole ya zo na biyu a hawan Derby), sannan ya lashe kofin gasar nadin sarautar taken Sarki George VI da Sarauniya Elizabeth da kofin nadin Sarauta a Royal Ascot.
"Ingarman Aureole a ko da yaushe kakkarfa ne da ke tinkahon cin gashin kansa, tare da harigidon kazar-kazar," a iya yadda take iya tunawa.
"Mafi yawan lokuta a kan bar shi sakaka (ba tare da dauri ba) a garin hada-hadar dawaki na Newmarket da lokacin horarwa, wannan shi ne dalilin da ya sanya ban cika damuwa da kubucewarsa a Ascot ba, a ranar da ya lashe kyautar Sarki George VI a wannan shekarar."
Aureole karamin doki ne, amma matashiyar godiya ta fi samun nasara a dawakai wajen daukar silikin Sarauta rawaya da kitson zinare da shimfidar hasken ja-ja da bakar hula mai kyalli, wadda aka kawata da silin zaren zinare.

Dawakan Sarauniya da suka samu nasarori

Asalin hoton, PA
1957: Carrozza, The Oaks
1958: Pall Mall, 2,000 Guineas
1974: Highclere, 1,000 Guineas
1977: Dunfermline, The Oaks
1977: Dunfermline, St Ledger

Daukacin launukansu duk mallakar mahaifinta ne Sarki George VI da kakan mahaifinta Edward VII.
A shekarar 1974, Dick Hern, wanda ya kasance mafi shaharar nagartar masu horarwa a zamaninsa, ya tura ingarman Sarauniya filly Highclere inda ya samu gagarumar nasarar lashe gasar sulallan zinare dubu (1,000 Guineas) a Newmarket.
Makonni shida daga bisani, wannan doki da Joe Mercer ya hau shi, sarauniya na kallo, ya lashe gasar Faransa ta Oaks a Chantilly.
Wannan ita ce mafi shaharar nasarar dawakan gidan sarauta, kuma nasarar lashe gasarar dawakan Sarauniya da suka kai ga makurar samun dimbin nasarori.
Mahayan managartan dawakan Willie Carson da Frankie Dettori sun yi ta samun dimbin nasarori; sai dai ba za a fifita su a kan Dunfermline, wanda ya lashe gasar cikarta shekara 25 a kan karagar mulki a shekarar 1977, wanda ya lashe daukacin gasar Oaks da ta St. Ledger.
Daukacin dawakan Dunfermline da Highdere sun samu horo ne a West Ilsley, wani wajen horar da dawakai da ke Berkshire, wanda Sarauniya ta saye shi a shekarar 1982.
Masu nasarar lashe gasa
A matsayinta na wadda ta mallaki katafariyar farfajiyar horarwa a fadin kasar, Sarauniya kan ziyarci dawakanta, inda takan nuna matukar sha'awarta da kaunarta na kiwo da horar da dawakanta.
Duk da kwarewarta da iliminta, ta takaita kanta ne wajen samun nasarar sukuwar dawaki a ''yan shekarun baya-bayan nan, daidai lokacin da gasar ke kasura ko bunkasa daga kan Larabawa da mutanen Irish da Amurkawa, masu dawakai da kiwonsu.
Sai dai babu tababa ta yi matukar tasirin bunkasa nagartar Birtaniyawa ta kafar bargar dawakin gidan sarauta (Royal Stud) a Sandringham, inda ta sako sababbin jini don kare martaba da inganta lamarin da ya damfaru a jininsu.

Asalin hoton, PA
Dawakai da dama sun ciwo wa Mai martaba dimbin nasarori, amma kasurar sha'awarta, ita ce wadda ta sayar a shekarar 1983, wato daga uwa zuwa Nashwan a wata Dabar masu nasara, kuma wadda aka tabbatar da cewa ita ce mafi kyawun tseren dawaki ta mil da rabi a tarihin tseren dawakai.
"A ko da yaushe ta fi sha'awar ingarman dokin da aka kebe don kiwo fiye da hakikanin tseren dawaki," a cewar Willie Carson.
"Zan iya fadar wani abu game da tseren dawaki, ita ma mai martaba Sarauniya ta fadi tamkar hakan."
Ko da yake ta lashe gasar tseren dawaki fiye da 600, ba ma a kasar Birtaniya ba, Sarauniya ta yi kasa warwas a mafi girman burinta. A daukacin tarihin Ingilishi, ingarma Derby ne kawai ya daure mata kai
Amma ingarman da ya lashe gasar shekarar 2005 - Motivator, mallakin bargar dawakin sarauta na Royal Ascot yana da alaka da gidan sarauta., don haka ya kasance tsayayye ingarman doki a Sandringham.
Dimbin gudunmuwarta
Bayan rasuwar mahaifiyarta Sarauniya ta gaji bargar dawaki
A shekarar 2009 ta halarci bikin al'ada na Cheltenham inda a karo na farko ta kalli dokinta, Barber's Shop, ya kammala zagaye na bakwai a gasar cin kofin zinare, wani dan taki tsakaninsa da tauraron gasar da babu mai kawar da shi, wato Kautp.
Sai dai an cika da farin ciki a gasar Kofin Zinare na shekarar 2013 da aka gudanar a Ascot, lokacin da karamin dokinta Filly Estimate ya koma gida, al'amarin da ya sanya Sarauniya ta kasance mai mulki ta farko da ke kan karaga da ta lashe gasar tun farkonta a shekarar 1807.

Asalin hoton, PA
An tsara yadda za ta bayar da kyauta ga wanda ya lashe gasar, amma sai ta samu cewa ita ce za ta karbi kofin da kanta, daga hannun danta, Basaraken Duke na York.
Mutumin da ya take mata baya, mahayin dokinta ne Ryan Moore. 'Ta lashe gasa da kyau, kuma yin hakan a wajen Sarauniya lamari ne mai kayatarwa. Lashe gasar kofin zinare na daga irin al'amuran da ke kayatar da ita, lamari jne da ba kasafai hakan kan kasance ba (al'amari ne na daban)."
Bayan murabus din godiya Estimate daga tseren dawaki sai aka mayar da ita bargar dawakin gidan sarauta na kiwo a Sandringham, inda ta yi haihuwar farko a shekarar 2016. Gudunmuwar Sarauniya a tseren dawaki, musamman kasancewarta mai kiwonsu ta kasance gagaruma.
Tabbas babu tababa kan irin kwazonta wajen tallafa wa wannan wasa, tare da irin farin cikin da take samu wajen kallon yadda ake gudanar da shi.
"Ko da yaushe mutum na samun zaburarwar kasadar caca," kamar yadda ta taba furtawa. "Burin cewa dokin mutum zai samu fifiko kan na wancan mutumin, shi ne dalilin da ke sanya wa mutum ya shigo a dama da shi.
©Hakkin mallakar dukkan hotunan abin kiyayewa ne












