Dangantakar Sarauniya Elizabeth da Firai Ministocinta

An wallafa

Matsayin Sarauta a kundin tsarin mulkin dimokuradiyyar zamani an kwatanta shi da babban aikin daidaito

Daga ikirarin Firai ministocin da ta yi aiki da su, ta bayyana karara Elizabeth II, baya ga cewa tana girmama takaitacciyar kimar da aka ba ta, ta samu ci gaba da bayar da gagarumar gudunmuwa a harkokin gwamnatin kasar nan.

A karkashin tsarin kundin mulkin Birtaniya da ba rubutattace ba ne ba, Basarake/Basarakiya (Sarki ko Sarauniya) na da hakkin a sanara da shi/ita komai ake ciki (na harkokin mulkin kasa), don bayar da shawara da yin gargadi.

A daukacin zamanin mulkinta, Sarauniya ta jajirce kan lallai a ba ta bayanin komai da komai game da duk wata matsayar harkokin mulki da gwamnatinta ta cimmawa, ita kuwa ba ta wani bata lokacin wajen bayar da shawarar da ra'ayinta a kebe, ga jerin Firayiministocin da suka yi aiki a zamaninta.

Matashiyar Sarauniya ta yi kyakkyawar sa'ar yadda aka nuna maka dabarun mulki a farkon zamanin mulki, inda ta samu agajin hamshakin dan siya, Winston Churchill, wanda ya sake samun damar jan ragamar mulkin bayan da aka gudanar da babban zaben shekarar 1951.

Wannan babban mutumin ya taba yin sharhi a kafar watsa labarai game da karfin ikon yarinyar Gimbiya al'amarin da ke da "ban mamaki a same shi a karamin yaro/yarinya."

Duk da bambancin shekarun da ke tsakaninsu - Churchill ya yi yakin Boer (Karon-battar Birtaniya da sojojin Transvaal na Afirka ta Kudu) zamanin mulkin kakar mahaifin Sarauniya, wato Sarauniya Victoria - dangantakarsu dai akwai kauna da girmamawa.

A jawabijn da ya gabatar nan take bayan darewar Elizabeth bisa karagar mulki, mya yi matukar daukar hankalin masu suararensa, inda ya furta cewa "ya fito da managarcin tsarin tabbatar da cewa Sarauniya ba za ta aikata wani abu da ba daidai ba."

Muhimmn lamura

Hakikanin dangantakar aiki tsakanin Basarakiya (Sarauniya) da Firayiminista babu cikakkiyar fahimta, sai dai wasu 'yan siyasa, musamman Disraeli da Sarauniya Victoria an nuna kwarewa karara fiye da wasu wajen nuna kyakkyawar mu'amala irin ta dangantakar aiki..

Mashahurin jagoran Jam'iyyar Conservative din nan, sabanin abokin adawarsa Gladstone, ba shi da wata tababa kan yadda zai tarairayi al'amuran huldar aiki da mai sarauta.

"Kowa na son kambamawar yabo," Disraeli ya fada. "Kuma idan ka je wajen harlkar sarauta sai ka bajeta karara a fili."

Abu guda mafi muhimmanci, shi ne, kowane Firai minista ya yarda da cewa Sarauniya jajirtacciya ce wajen aiki.

Takan shafe kimanin sa'o'i uku a rana wajen bibiyar sakonnin takardun majalisa da sakonnin gwamnati da bayanan sassan harkokin mulki da nade-naden mukamai.

Wasu da sauran al'amura akan bijiro da su ne lokacin da Firayiminista ya je Fada don suararen bayanan mako-mako.

Wasu lokutan akan gabatar da suararen bayanan ne a wani wuri daban. Lokacin zamanta a Balmoral a karshen dogon hutun bazara, shi ne mafi muhimmancin isar da sako ga Firayiminista a shekara.

A gaskiya, babu wnai tanadi a kundin tsarin mulki da ya bayar da damar irin wannan ganawar, kawai dai lamari ne da ya dnganci al'ada. Wasu lokutan tattaunawar wayar tarho kan maye gurbin ganawar keke-da-keke.

Tashin farko, lamarin na nuni da cewa, kaifin basirar Sarauniya da kwarewarta a harkar siyasa lamura ne da ke burge mazaunan fadar Firayiministar kasa da ke Lamba 10 (titin Dawning).

Watsi da kimar matsayi

An yaba yadda take iya yin takun tarairayar kimar matsayin mukaminta bisa tanadin kundin tsarin mulki, baya ma ga a ce lokacin da aka wsamu rudanin siyasa a shekarar 1957, har ta kai ga Anthony eden ya yi murabus daga Firayiminista sanadiyyar rikicin mashigin ruwan Suez (a Masar - takun sakar yakin Larabawa da Isra'ila).

A wancan lokacin Jam'iyyar Conservative ba ta da wani tsari na zaben sabon shugaba, ta yadda a kodayaushe ake dogaro da samun mutum nagari "sakaka."

Bayan da Sarauniya ta tuntubi Churchill don neman shawara, sai ta bukaci Harold Macmillan ya kafa gwamnati, al'amarin da mamakinsa ya shammaci dimbin masu sharhi kan al'amura, wadanda suka sa ran ganin mataimakinsa na bayan fage "Rab" mai hidima, ya dare bisa mukamin.

Ta fuskanci irin wannan matsalar shekaru kadan kawai sa'adda Macmillan ya yi murabus, bisa dalilin rashin lafiya. Duk da irin matsalolin da murabus din Eden ya haifar Jam'iyyar Conservative zuwa lokacin ba ta yi tanadin tsarin zaben shugaba ba. Bayan da ta tuntubi Macmillan a gadonsa na asibiti, inda yake jinya, sai ta sa aka kirawo Earl of Home (Dan majalisar manyan mutane a cikin al'umma da ke taro a fadar Sarauniya).

Kasancewar ba a taba yin Firayiministan Birtaniya daga Majalisar manyan mutanen kasa (House of Lords) tun daga shekarar 1902, kuma ana ganin tsari da ba za a amince da shi ba. Don haka sai ya yi watsi da kimar matsayinsa, ya kuma samu nasara a zaben cike gurbi, inda daga bisani ya dawo a matsayin Sa Alec Douglas-Home.

Ba a samu sauyi ba har zuwa shekarar 1965 sannan 'yan Jam'iyyar Conservative suka fito da tsarin zaben shugaba, ta yadda nan gaba ba za su sake jefa Sarauniya cikin matsala ba.

'Harzukar al'umma'

A shekarar 1964 Harold Wilson ya kasance Firayiministan farko na jam'iyyar Labour da ya yi aiki da sarauniya, wanda ya sha caccakar sukar lamiri daga 'yan majalisarsa kan shirin kara yawan kudin da gwamnati ke bayarwa na tafiyar da aikace-aikacen ofishin Sarauniya.

Sai dai kamar yadda Barbara Castle, daya daga manyan ministocin Mista Wilson ke iya tunawa, Firayiministan da Sarauniya sun hada karfi don kawar da kowace irin tashintashinar da ka iya tasowa.

"Harold na kaunar Saruniya," a cewarta. Kuma shi shugaba ne mai wayo, shi ya sa ma yake da fahimtar cewa tashintashina na iya bijirowa ta harzuka al'umma su soki Sarauniya."

Bayan tattaunawar Mista Wilson da Sarauniya kan yadda al'umma ta harzuka, sai ta amince da cewa za ta dauki nauyin wani yanki na kudin da za a kara a kashin kanta.

Kasancewar an sake zuba wa kimar matsayin Sarauniya a kundin tsarin mulki ido bayan da masu hakar ma'adanai suka baro da Gwmanatin Edward Heath a shekarar 1974. Sai ya dan rike madafun ikon na wasu ''yan kwanaki, da zimmar ganin ya sake kafa wata sabuwar gwamnati

Rahotanni daga fada sun yi nuni da cewa Sarauniya ba ta ji dadin wannan yanayin na rashin tabbas ba, kodayake Heath da kansa ya fayyace cewa babu wata tuntuba da aka yi masa.

Dangantakar aiki da Firayiminista mace ta farko a Birtaniya, Margret Thatcher, ba kodayaushe lamari ya yi dadi ba, musamman kan takaddamar kungiyar kasashe rainon Birtaniya ta 'Commonwealth.'

Yamutsi

Thatcher kadai ce a cikin shugabannin kungiyar kasashen rainon Birtaniya dage wajen kin amincewa a kakaba wa Gwamnatin wariyar launin fata ta Afirka ta Kudu takunkumi bisa dalilin cewa ba zai yi tasiri ba, kuma illar lamarimn za ta cutar da mutane matalauta ne.

A shekarar 1986 jaridar Sunday Times ta ruwaito cewa Sarauniya ta fahimci cewa halayyarta (Magret Thatcher) salo ne na hantarar karo da juna, lamarin da ke da "daure kai."

A al'adance, matsayin Sarauniya shi ne na mai bayar da shawara ga Firayiminista. Amma a 'yan shekarun baya-bayan nan, kimar matsayin an kawar da shi.

John Major ya samu kasansa a matsayin amintaccen mashawarci kan al'amuran da al''umma ba su san inda aka sa gaba ba, game da iyalan gidan Sarauta, kamar al'amuran da suka shafi rabuwar auren Yarima da Gimbiyar Walse.

Amma ko da bayan lokacin yamutsin da Sarauniya ta shiga, tsohon shugaban jam'iyyar Conservative ya tauye mata damarta, wadda to kowace fuska an dakileta, sannan ya bayyana yadda yake daukar shawar Sarauniya da matukar kimar muhimmanci.

Akwai lokacin da Sarauniya ta ji cewa al'umma sun fara ja-baya da ita.

An zargeta da rashin yin katabus lokacin da kasar ke cikin alhinin rashin Diana, Gimbiyar Wales, a shekarar 1997, kodayake tana da tabbacin cewa, a matsayinta na kaka, aikinta shi ne ta kebe kanta don kwantar da hankalin kananan 'ya'yan Diana.

Rashin matsayar majalisa

A wannan yanayi, mutumin da ya fahimci yadda kafafen yada labarai ke juya akalar al'amura, Tony Blair, shi ne ya bayar da managarciyar shawara, kuma kai tsaye ya dauki hankalin al'umma da kalamansa game da "Gimbiyar al'umma."

An kuma ruwaito cewa Blair ne ya kasance a gaba-gaba wajen shawo kan Sarauniya ta baro Balmoral ta koma Landan sanadiyyar tursasawar labaran 'yan jarida.

A shekarar 2007 Gordon Brown ne ya gaji Blair, wanda ya sha kayi a shekarar 2010 al'amarin da ya jefa dimokuradiyyar Birtaniya cikin mawuyacin hali.

Akwai hasashen rashin cimma matsayar majalisar dokokin kasa kafin a fara zabe, wato idan aka samu babu jam'iyyar da ke da rinjaye (me ya kamata ayi?).

Tuni dai aka yi tsarin da ya kare Sarauniya daga afkawa rudanin siyasa. Sai dai ta bayyana karara cewa za a rika ba ta cikakkun bayanai lokacin da takaddamar ke gudana bayan kammala zabe a karshen mako.

Bayan murabus din Brown ne kawai, sai Jam'iyyar Conservative ta yi hadin gwiwa da jam'iyyar Liberal Democrats, har ta kai ga an nemo David Cameron zuwa fada, inda aka bukaci ya kafa gwamnati.

Rashin yarda

Ya ce ya fahimci fa'idar da ke tattare da tattauna matsaloli da wanda ke gefen tsarin siyasa "da matukar muhimmanci."

"Ba ni da tabbaci cewa kodayaushe akwai dimbin alfanu (fa'ida mai yawa), amma akwai fa'ida mai yawa a gareni," a cewarsa, "Saboda na fahimci yana taimaka mana wajen tantance matsaloli da ke damfare cikin kaina kan abin da muke bukatar yi."

A babban zaben 2015, David Cameron ya samu kuri'u masu rinjaye, al'amarin da ya ba shi damar komawa gidan Gwamnati da ke titin Dawning a matsayin Firayiminista.

Sai dai wa'adin mulkinsa takaitacce ne. Cikin Yunin shekarar 2016 al'ummar Birtaniya sun ki yarda da da shawararsa, inda suka zabi ficewa daga Tarayyar Turai (EU).

Cameron ya sanar da murabus dinsa a matsayin Shugaban Jam'iyyar Conservative, bayan da aka kada kuri'un aka fara shirye-shgiryen zaben magajinsa, al'amarin da aka tsara aiwatarwa cikin watanni uku.

Kodayake an yi watsi da tsarin cikin kankanen lokaci, bayan da aka fitar da 'yan takara biyu, wato Andreal Leadson, wanda ya fice daga takarar, ya bar Theresa May ta zama sabuwar shugaba.

Ranar 13 ga Yulin 2016 ta je fadar Buckingham don Sarauniya ta bijiro mata da bukatar kafa sabuwar gwamnati. Ita ce Firayiminista mace ta biyu da ta yi aiki da Sarauniya, kuma ta 13 a jerin wadanda suka yi shugabancin kasar a zamaninta.

Harold Wilson, wanda ya yi zango uku na wa'di mulki a fadar Gwmanati da ke lamba 10 na titin Dawning, ya taba cure bayanin fa'idar da ke tattare da dangantakar aiki tsakanin Firayiminista da Shugabar kasa (Sarauniya).

"Gaskiyar lamari ita ce akwai mutum daban a gefe da bai damfaru (da hada-hadar siyasa ba), wanda damuwarsa/ta kawai ita ce majalisar dokoki ta cimma matsaya daidai da bukatar mutanenta. Wannan shi ne abin da kawai babu a kasashen da ke kan tafarkin tsarin shugabannin kasashe."

©Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka