Sauyin da aka samu a masarautar Burtaniya karkashin mulkin Sarauniya

Queen Elizabeth II accompanied by Prince Philip waves to the crowd, 02 June 1953

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An haifeta a zamanin ban girma da tsauraran dokokin fada, al'amuran da suka wanzu matuka gaya a karni na 19 fiye da na 20
An wallafa

Zamanin mulkin Sarauniya ya bijiro mata da sauye-sauye iri-iri a dangantakarta huldarta da mutane.

Karfin halin Sarauniya Elizabeth ne ya sanya ta tabbatar da cewa akwai bukatar sauya fasalin al'amura, domin jin akwai yiwuwar juyin-juya halin salon zamantakewar al'umma da ke gudana a wajen kofofin shiga fadarta.

An haifeta a zamanin ban girma da tsauraran dokokin fada, al'amuran da suka wanzu matuka gaya a karni na 19 fiye da na 20.

Duk da tashin-tashinar kashe-kashe na babban yaki, al'ummar Birtaniya har yanzu kimar yawan dukiya da matsayin mukami na da tasiri.

Dokokin tafiyar harkokin sarauta, tare da dangantakar sarauta da mutanen waje, suna da tsauri, kuma ana ganin da wuya a sauya su.

A shop assistant in a butcher's shop in south London cuts a coupon out of a customer's ration book on the first day of rationing in Britain

Asalin hoton, Getty Images

White Line 1 Pixel

A lokacin da ta kama ragamar mulki, mafi yawan taswirar duniya an shafeta da launin ja, wato gadon daular mulki da aka yi rugu-rugu da ita, amma ba a lalata gaba daya ba, sanadiyyar yakin duniya na biyu.

Ta hau gadon sarauta tana matshiyar mace mai karfin hali, in an kwatantata da mazan da shekarunsu suka tasa, a cikin gida da kasashen waje.

An yi ta magana kan sabon zamanin Elizabeth, kamar yadda Sa Winston Churchill ya yi nuni kan hakan, al'amarin da ya yi kafada-da-kafada da cire sasarin tsuke aljihun gwamnati bayan kammala yaki.

Makomar sarauta ta samu cikakkiyar kariya. Kowace irin suka daga rukunin masu akidar zaben shugaba (ta hanyar kada kuri'a a dimokuradiyya) ko masu adawa da sarauta an kebe su a can gefen harkokin siyasa.

Abin da ba zai yiwu ba

Amma a shekarar 1957 al'umma ta yi ta tafka muhawara kan matsayin sarauta a zamanin wayewar kai, kuma ko tantama babu lamarin ya kunno kai daga wanda ya gaji kimar matsayi a jam'iyyar Conservative.

Lord Altrincham, wanda daga bisani ya yi watsi da kimar matsayinsa ya koma sakayau kawai wato John Grigg, ya rubuta wata makala a mujallar Ingilishi ta kasa (National and English Review ) ta kwararru, wadda ba ta cika kewayawa ba sosai ba.

A cikinta, ya yi magana kan matashiyar Sarauniya cewa, "munin lamarin rashin samun cikakken horo" wannan aiki, inda ya yi nuni da irin salon maganarta a matsayin "cukurkudadden lamari", kuma ya ce kimar mutuntakarta na nuni da "natsattsiyar 'yar kwalisar 'yar makaranta da ke ji-ji-da-kai."

Picture shows (l-r) Roy Kinnear, David Frost and Lance Percival
White Line 1 Pixel

Dangane da sarauta, cewa ya yi, za ta tunkari "lamarin da ba zai sabu ba, wato lokaci guda na kara-zube da kimar mukamin matsayi na daban."

Caccakar ntashintashintar da ta biyo bayan fitowar makalar ta bayyana bambamcin da ke tsakanin al'umma game da yadda suka dauki salon sarauta.

Altrincham ya yi ikirarin cewa makalarsa an yi ta ne "ba da wata manufa ba fiye da hidima ga tsarin sarauta, don karfafata, sannan a tabbatar da dorewarta. Don tana da kimar kyawun tasirin da ba ta kamata a yi watsi da ita ba."

Kiran da aka yi na "hakikanin rashin matsayi da Kotun kasashen rainon Birtaniya na Commonwealth" da fargabarsa kan yadda ake ilimantar da Yarima Charles, masu kaunar sarauta sun kashe bakin tsanya (watsi da batutuwan da aka bijiro da su).

Hantara

Altrincham ya sha tsokana da hantara a titi a hannun masu kaunar daular mulkin sarauta, daidai lokacin da fito daga dakin shirye-shiryen talabijin.

Amma dai makalarsa ta yi tasiri jan ra'yin mutane suka fara jefa alamar tambaya game da tsaurara al'amuran da ke jan ragamar kasar.

Sai masu shekaru 60 da doriya suka fara bude sabon babi. Sai matasan da a da jinsu kawai ake yi ba a ganinsu suka fara bayyana a fili ta kafar suturu da tsarin rayuwa da kade-kade da raye-raye.

Prince Philip and the Queen on board a plane

Shirye-shirye irin su Wannan makon ne da babu tausayi (That Was The Week That Was mercilessly) ya rika caccakar manya da managarta, yayin da abin kunya da ke tattare da lalatar babban mutum da 'yar kwalisar tallata haja ta jawo m,utane suka rika ganin cewa sarauta ma ba ta da kariya.

Abu na biyu kuwa, matsayin Sarauniya na shugabancin kungiyar kasashe rainon Birtaniya ya kara kimar daraja yayin kasashen da ke karkashin mulkin mallaka suka yi ta samun 'yancin kansu.

Share martaba ta daban

A samu ziyarce-ziyarce ba kakkautawa a kasashen da suka dade da sababbin da suka shigo kungiyar rainon Birtaniya, kuma Sarauniya ta yi kokari na musamman wajen karfafa tattauna da hadin gwiwa dangantaka tsakanin kasashe masu arziki da masu tasowa.

A Yunin 1969 wani shirin kundin bayanai na BBC mai taken Iyalanb gidan Sarauta ya fayyace wa mutane wata mahanga sabanin yadda a da suke kallon sarauta.

An ga Sarauniya a bakin aiki da wajen was, inda take bayani a Fadar Buckingham da halartar taron jami'an diflomasiyar kasshen waje da yadda take shakatawa tare da iyalanta a Balmoral, al'amuran da suka hada da lamura masu kayatarwa da za a yi ta tunawa, kamar yadda take a wajen gasa nama.

Queen Elizabeth II crowns her son Charles, Prince of Wales, during his investiture ceremony at Caernarvon Castle, 1 July 1969

Asalin hoton, Fox Photos / Getty Images

Bayanan hoto, Ba kowa ne ya yi maraba da sabon Yariman Wales ba

Sai dai bude waznnan kafa ba kowane ya dadin yin hakan ba. Domin wasu fadawa da masu bayar da shawara a fada na da tabbacin cewa bude babbar kafa ga kafofin yada labarai, jigon lamarin da ke tattare da Iyalan gidan sarauta, kimar martaba ta daban an yakiceta.

Wannan sabon salon bude kafa an fi alakanta shi da kawun basaraken Duke na Edinburgh, Lord Mountbatten na Burma.

Irin fahimtarsa kan yadda Iyalan gidan sarauta ya kamata su zamo, an yi masa lakabin salon Mountbatten - ko a Ingilishi -"Mountbattenism", lamarin da marubucin tarihin Sarauniya, Ben Pimlott ya bayyana a takaice da " zaburarwar jan ra'ayin al'umma."

Bukukuwan da suka hada da kaddamar da sarautar Yarima na Wales a gidan sarautar Caenarfon a shekarar 1969 da bikin cikar sarauniya shekara 25 a karaga cikin shekarar 1977, duk an yi su ne da manufar nuna cewa masu sarauta daidai suke da mutane.

Kimar darajar mutuntaka

Duk da dimbin nasarorin da aka samu, wasu 'yan yankin Welsh da ke da akidar 'yan kasanci sun yi mummunar sukar lamirin bikin da aka gabatar.

Wannan yaye rufin da ya kange su ya tafi kafada-da-kafada da sauye-sauyen tsarin hada-hadar kashe kudin Iyalan gidan Sarauta.

Yawan kudin da majalisar kasar ke biya don gudanar da ayyukan Sarauniya an rage shi, inda Sarauniya ta fara biyan haraji kan kudin da take samu daga jarin da ta zuba a harkokin kasuwanci, kuma an yi matukar rage yawan kudin da take kashewa wajen gudanar da harkokin gidanta.

York, Duchess Sarah Ferguson, Edward, prince, Anne, Princess Royal and Andrew, Prince during Its A Royal Knockout and Aled Jones in the foreground

Asalin hoton, Photographers International

Abin takaicin shi ne matasan gidan sarauta babu wani katabus da suka yi wajen farfado da kimar martarbar mutuntakar sarauta.

Yayan sarauniya uku daga cikin hudu sun sajmu matsalar watsewar aurensu, tare da al'amuran da suka hada Sarauta ta rusa kanta, sun kara rage goyon bayan al'umma ga masu mulkin sarauta.

Sanadiyyar takaddamar da aka tafka kan ko wa zai biya asarar da aka tafka a gobarar gidan sarauta na Windsor, Iyalan gidan sarauta sun yanke matsayar bayar da gudunmuwa wajen kawo ci gaban muhawarar a zamance.

Rukunin masu neman mafi na The Way Ahead group, wanda ya kunshi 'yan gidan sarauta da manyan fadawa, an yanke cewa za su su rika haduwa domn tattaunawa sau biyu a shekara.

Masu Sukar lamiri

Jerin al'amuran da rukunin masu neman mafitar za su rika tattaunawa a kai sun hada da makomar sarauta da mkudin gudanar da harkokin sarauta, tare da yadda za a jawo ra'ayin al'umma su yi wa sarauta kyakkyawar fahimta.

Duk da cewa sun yi kokarin kaucewa l'amuran tashin hankali a kasar, Iyalan gidan sarauta sun yi fama da sukar lamiri daga al'umma bayan mutuwar Diana, Gimbiyar Wales a Agustan 1997.

Sauraniya da ke hutunta na bazara a Balmoral da ke Scotland, ta sha suka saboda kin dawowarta Landan ko yi wa al'umma ta'aziyyar surukarta da suka rabu da danta.

Crowds at Princess Diana's funeral

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, An ga dumbin jama'a a ranar jana'izar Gimbiya Diana a kan tituna

Abin da masu sukarta suka kasa fahimta, shi ne, Sarauniya a matsayinta na kaka mai nuna kula, ta ji cewa kamata ya yi ta killace kananan ''ya'yan Diana daga idon al'umma, ta yadda za su yi jimamin rashin cikin gidanbsu a kebe.

Dimbin mutane sun yi watsi da al'adar Birtaniya da ta taso a cikinta, inda suka koma barkwancin alhini.

Bayan da wata jarida ta yi t akambama kiraye-kirayen ganin Sarauniya ta dawo Landan, inda ta yi jawabi kaitsaye aka watsa ta talabijin, inda t ayi ta'aziyyar tsohuwar surukarta.

Shigowar sabon karni zai ci gaba da bijiro da sauye-sauye ga tsarin sarauta.

Nuna kauna

Muhimman ranaku - su ne na hada-hadar kasuwnaci da yada labarai da ayyukan fasaha sun kasance ana aiwatar da su, inda suka hada da kai ziyarce-ziyarce a birnin da bayyana a shirin BBC EastEnders.

Lamarin da ya fi "sosa-zukata" sarauta ta kafu kn turbar mabambantan al'adun Birtaniyawa da addinai.

Ta yiwu ma'auni mafi kyau na dabarun cin nasarar goyon bayan al'umma, shi ne bukukuwan da aka gudanar na cikarta a karaga shekaru 50 cikin shekarar 2002 da na cikarta shekaru 60 a karaga, wanda aka gudanar shekaru 10 da suka gabata.

Buckingham Palace during the Trooping the Colour, 2015

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Makamomar masarautar ba ta fuskantar barazana

Miliyoyin mutane sun fito a daukacin bukukuwan lokacin da Sarauniya take kewaya kasar Birtaniya, inda aka nuna kauna a fili ga sarauniya.

Lokacin da aka haifi mashahurin tattaba kunnenta Yarima George na Cambridge a shekarar 2013, lamarin tamkar cankar cacar tabbatar da cewa zai gaji sarauta, ana dai kara ganin lamarin tamfar kariya ce.

Ko wadanne irin sauye-sauye suka faru a cukurkudaddiyar dangantakar sarauta da mutane, al'amarin da ya bayyana karara, shi ne har yanzu al'umma na karfafa nuna goyon baya ga Sarauniya.

A wajen mutane da dama, har yanzu ita ce mai bayar da tabbaci ga al'umma a Birtaniya, wadda ta yi matukar sauya tun daga zamanin da ta kama ragamar mulki.

Tare da tallafin Basaraken Duke na Edinburgh, Basarakiyar Birtaniya mafi dadewa a karagar mulki, ta samu nasarar juya akalar sarauta, inda ta kai ga gaci zuwa karni na 21.

©Dukkan hotunan na da hakkin mallaka