Jarumin Bollywood Kader Khan ya rasu yana da shekara 81 a duniya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Fitattacen jarumin fina-finan Bollywood, Kader Khan, ya rasu yana da shekara 81 a duniya.

Rahotanni daga India sun ce ya rasu ne a asibitin Canada bayan ya dade yana fama da wata rashin lafiya da ta shafi kwakwalwa.

Kader Khan wanda musulmi ne ya fito a fina-finai sama da 300 na Bollywood a tsawon rayuwarsa.

Tun a 1973 ya fara fim inda ya fito a wani fim mai taken 'Daag' tare da shi da Rajesh Khanna da Sharmila Tagore.

Yana fitowa a matsayin bos da kuma uba kafin ya koma yana wasan barkwanci a wajajen 1990.

Kader Khan ya dade yana rubuta labarin fina-finai kafin ya fara fitowa a fim.

Ya rubuta labarin fina-finai da dama da suka yi fice, kamar 'Coolie' da 'Amar Akbar' da 'Mukaddar Ka Sikandar.'

A birnin Kabul na Afghanistan aka haifi Kader Khan, daga baya iyayensa suka koma Mumbai yana karami.

Abokan aikinsa a harakar fina-finansa da dama ne suka bayyana alhinin rashin Kader Khan.

Fitaccen jarumin fina-finan Bollywood Amitabh Bachchan ya bayyana rasuwar Kader Khan a matsayin babban rashi inda ya ce ya samu nasarori a basirar fina-finansa da ya rubuta.

Haka ma, Abhishek Bachchan dan Amitabh Bachchan ya wallafa sakon ta'aziyarsa ga iyalan Kader Khan inda ya ce ya samu damar yin aiki tare da shi.

Daya daga cikin wadanda suka yi zamani da Kader Khan Shatrugan Sinha ya bayyana Kader Khan a matsayin wanda babu kamarsa.

Shi ma Akshay Kumar daya daga cikin fitattun jaruman Bollywood ya bayyana alhininsa a Twitter inda ya ce sun yi aiki tare sosai a fina-finai da dama tare da jajantawa iyalansa.

Kader Khan ya mutu ya bar matansa daya Azra da 'ya'ya biyu Sarfaraz da Shahnawaz, wadanda jarumai ne a fina-finan Bollywood.