Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tsunami da amon wuta sun afka wa Indonesia
Jami'ai a Inodonesia sun ce mutum 40 ne akalla suka mutu lokacin da iftila'in tsunami ya auka wa gabobin teku da dama a kewayen mashigar ruwan Sunda, zirin tekun da ya raba tsibiran Java da Sumatra.
Hukumar dakile aukuwar annoba a ce kusan mutum 600 ne suka ji raunuka karin wasu kuma har yanzu ba a san inda suka shiga ba.
Har yanzu ayyukan agajin gaggawa ba su kai ga yankunan da abin ya shafa ba.
Hukumomi na gudanar da bincike a kan ko girgizar da dutsen Anak Krakatau mai amon wuta ya yi ce ta janyo tsunami.
Aman da dutsen Krakatau ya yi a karshe karni na 19, na daya daga cikin al'amari mafi haddasa mace-mace da rugujewar gine-gine a tarihi.