Fashewar bututun mai ya hallaka mutum 16 a Aba

An wallafa

Rahotannin daga birnin Aba da ke yankin kudu maso gabashin Najeriya na cewa akalla mutum 16 sun rasa rayukansu bayan da wasu bututun mai biyu suka fashe a jiya Jumma'a.

Jami'ai a birnin sun ce lamarin ya biyo bayan ayyukan barayin man fetur ne masu fasa bututun man domin satarsa.

Wadannan bututun man na samar wa yankin na Aba da kewaye da mai daga wata matar mai da ke yankin Neja Delta mai arzikin man fetur.

Wadanda suka gane wa idansu al'amarin sun bayyana ganin jami'an lafiya na kawar da konannun gawarwakin wadanda iftila'in ya rutsa da su a birnin Aba, wanda shi ne cibiyar kasuwanci a yankin.

Jami'an hukumar tsaro ta cikin gida, NSCDC, sun bayyana cewa fashewar farko ta janyo rasa rayuka 12, wadanda suka hada da wasu matan unguwar, kana mutum hudu sun mutu daga baya a yayin da bututu na biyu ya fashe kusa da na farko.

Amma wasu rahotannin na cewa wadanda suka mutun sunzarce 30, kuma gomman mutanen sun sami kuna, inda wasu gine-ginen da ke kusa sun kone kurmus.

Kamfanin mai mallakin gwamnatin Najeriya, NNPC, ya alakanta fashewar bututun biyu ga ayyukan barayin mai, kuma tuni ma'aikatan kashe gobara suka killace wurin.