Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Najeriya: Mutum 35 sun mutu a gobara
An wallafa
Mutum 35 aka tabbatar da mutuwarsu a wata gobara da iskar gas ta haddasa a garin Lafiya na jihar Nassarawa, yayin da wasu daruruwa suka samu rauninka.
Rahotanni sun ce wata tankar dakon gas ce ta kama da wuta a wani gidan man Natson da ke kan babban titin da ya hada Abuja da Arewaci da kuma kudancin kasar.
Kuma wutar ba ta tsaya a anan kadai ba, domin ta kona motocin da ke ajiye a bakin hanya da kuma masu wucewa, da kuma kona shaguna da dama
Gobarar ta tayar da hankalin mazauna yankin da abin ya shafa.
Mutanen da gobarar ta rutsa dasu sun samu munanan kuna.