Uwargidan Trump, Melania ta fara ziyara a Afirka

This file photo taken on June 06, 2016 shows Melania Trump, wife of Republican presidential candidate Donald Trump, listening as her husband delivers remarks at Trump National Golf Club Westchester in Briarcliff Manor, New York.

Asalin hoton, AFP

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Matar shugaban kasar Amurka, Melania Trump ta fara ziyarar yinin biyu a Ghana inda ta hadu da takwararta Ghanar, Rebecca Akufo Ado.

Ghana ita ce kasa ta farko da za ta fara yada zango a rangadin kasashe Afirka hudu da take yi da suka hada da Malawi da Kenya da kuma Masar.

Wannan shi ne karon farko da Mrs Trump ta ke wakiltar gwamnatin mijinta a ziyarar da ta kai ita kadai.

Ziyarar tata dai za ta mayar da hankali ne kan bunkasa manufar kiwon lafiya da ilimi da hukumar agaji ta Amurka USAID ke tafiyar da su.

Za kuma ta ziyarci Kenya da Malawi da Masar ne don karfafa dangantakar diflomasiyya.

A watan Fabrairu wani ce-ce-ku-ce ya barke bayan da aka yi zargin cewa Shugaba Donald Trump ya bayyana kasashen Afirka da cewa "kasashen banza ne."

Ana ganin ziyarar ta uwargidan Trump a matsayin wani mataki na taimakawa wajen magance rarrabuwar kawunan.

Za kuma ta tallata wani shirinta na Be Best wanda aka kirkira don magance cin zarafi a intanet da kuma inganta kiwon lafiya.

Ta wallafa a shafinta na Twitter cewa shirin nata zai bazu a kasashen duniya.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Mrs Trump ta ce yayin ziyarar tata, tana sa ran zuwa kyawawan kasashen Afirka hudu.

Daraktar watsa labaranta Stephanie Grisham ta ce: "Tana sha'awar Afirka ne saboda ba ta taba zuwa nahiyar ba, don haka ta san kowace kasa tana da nata salon al'adar da kuma tarihi."

Mene ne tunanin Donald Trump game da Afirka?

Shugaba Donald Trump wanda ke yawan amfani da Twitter a matsayin babbar hanyar sanar da manufofinsa ya yi amfani da kalmar Afrika ne kawai a wani sakon Twitter a watan Agusta.

Yana mayar da martani ne a wani rahoto na gidan talbijin na Fox News da ya yi ikirarin cewa ana yawan kashe Turawa manoma.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2