Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sarauniya Elizabeth II: Waiwaye kan gudunmawar Sarauniyar Ingila da Commonwealth
Lokacin da Sarauniya Elizabeth II ta hau karaga a 1952, Daular Birtaniya na nan daram
Yayin da kasar Indiya, mai lakabin "kawar adon kambin sarauta," ta samu 'yanci, daukacin taswirar duniya na damfare da launin ja.
Shekaru 20 da suka biyo baya an yi ta sauke tutar Birtaniya a kasashe da dama, wadanda suka kasance karkashin mulkin mallakarta a da, inda suka samu 'yanci.
Mafi yawan sababbin shugabannin kasashen rainon Birtaniya tsararrakin Sarauniya ne, don haka ta sansu, tare da dimbim matsalolinsu.
Matsayinta ya zama tambarin daidaiton adalcin hadin kai, da ke wakiltar kasashen rainon Ingila ke son cimmawa.
Sarauniyar ta fayyace irin matsayin ta hanyar nuni da ra'ayinta na son huldar aiki tare da kungiyar.
A cewar Sir Shridath "Sonny" Ramphal, Sakatare-Janar na kungiyar Commonwealth tun daga 1975 zuwa 1979: ta sarayar da rayuwarta da dabararta tarbiyyart tare da dangantakarta, wajen nuna halin kula ga kungiyar kasashen rainon Ingila ta Commonwealth."
Sakamakon haka Mai martaba Sarauniya ta samu kimar darajar mutuntaka.
"Sarauniya ta kasance wani babban al'amari da ya samu kungiyar Commonwealth," a cewar tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo a shekarar 2002.
Muhimmiyar ganawa
"Ta kasance babbar jigon daidaita al'amura da ban mamaki, ga ta mace mai abin mamaki."
Sarauniya ta ziyarci daukacin kasashen da ke kungiyar rainon Birtaniya ta Commonwealth a kalla sau daya, inda ta fara kai ziyarar rangadi a kasashen Austiraliya da New Zealand a shekarar farko da hawanta karagar mulki.
Sannan ta fito da tsarin ganawa da shugabanin Commonwealth, inda ake gayyatarsu halartar wata takaitaciyar ganawa a bainar jama'a bayan shekaru bibiyu.
"Takan gana da kowane shugaban gwamnati a tsakanin mintuna 20 zuwa 30 a kebe," kamar yadda Sonny Ramphal zai iya tunawa.
"Ko da yaushe ana bata managarcin bayani a takaice. Sai dai 'yan Republican ko shugabanni masu tsattsauran ra'ayi sukan kasance, sun tabbatar da cewa ganawa da Sarauniya muhimin al'amari ne."
A matsayin Sarauniya na shugabar je-ka-na-yi-ka ba ta da karfin iko. Amma dai tana da tasiri.
Idan shugabanni suka zo mata da matsaloli, a wasu lokuta takan dora su kan hanyar da za a samu warwarar matsalar. Sarki Mswati III na Swaziland zai iya tuna al'amura da dama da suka faru.
Rabuwar kai
"Takan karfafi gwiwar dimbin mutanen da muke bukatar gani kan wata matsala da muke gabatar mata, ko wani abu mai kama da haka.
Daga nan sai mutanen da muke bukatar gani sai su yi wani dan yunkuri."
Kimar hadin kan Sarauniya an sha gwada su a lokuta da dama tun gabanin taron shugabannin kungiyar kasashen Commonwealth da aka gudanar a Babban birnin Zambiya Lusaka cikin shekarar 1979.
Ta sha matukar wahala ganin yadda Firayiministarta Margaret Thatcher ta shiga rikici da mafi yawan shugabannin kasashen kungiyar Commonwealth kan yadda ta ki amincewa a kakaba wa Afirka ta Kudu takunkumi.
Haka kuma a lokacin da makomar kasar da a da ake kira Rhodesia ya haifar da rabuwar kawuna a tsakanin shugabannin kungiyar Commonwealth.
Sojojin Ian Smith sun yi luguden bama-bamai kan sansanin 'yan adawa da ke Lusaka kwanaki kadan gabanin taron.
Matakin da ya dauka ya bai wa wasu shugabannin damar yin uzuri, musamman Robert Muldoon na New Zealand, wanda ya roki Sarauniya ka da ta halarci taron. Amma, a kamar yadda Sonny Ramphal ya tuna cewa, ta yi matukar jajircewa.
"Ta bayyana wa shugabannin karara da daukacin Firayiministan kasashen, farare da bakake, tsofaffi da sababbi cewa ba za a raba kungiyar Comonwealth ba, dole ne kungiyar ta Commonwealth ta cimma matsayar daidaita al'amura cikin lumana.
Nasarori
"Hakika wannan shi ne kimar karfin tasirinta da kimar mutuncinta da ake gani."
Sarauniya ta yi aiki tukuru wajen cimma yarjejeniyar zaman lafiya kan al'amarin da mafi yawan mutane ke ganin shi ne lokaci mafi kyawunlamari ga kungiyar Commonwealth.
Duk da irin jajircewarta kan kungiyar Commonwealth, kungiyar ba ta kasance ba face 'yar ku ci, ku ba mu kan harkokin duniya, in an kwatantata da kungiyoyi ko hukumomi masu karfi, wadanda suka hada Asusun Lamuni na duniya 'IMF' da Bankin Duniya.
Nasarorin da tacimmawa sun kasance kimarsu ba ta da girma a fanonin da suka hada da al'adu da kimiyya da ilimi. Sannan da kafar tattaunawa tsakanin Arewa da Kudu.
Makomar shugaban kungiyar Commonwalth ba a san inda ya nufa ba. Domin jagora bai cika zama shugaba ba, kaitsaye, kuma wasu kan iya bijiro da alamar tambaya kan jajircewar sabon Sarki game da kungiyar.
Sannan babu wata masaniya kan cewa mutuwar Sarauniya na iya haifar da kasurar tsarin jamhuriya na zaben shugabanni (Repubicanism) a wasu kasashen da har yanzu sarautar Birtaniya ke jan ragamar shugancin kasashen.
Masu adawa da sarauta a Austiraliya, alal misali suna da tabbacin cewa mutuwar Sarauniya za ta bayar damar gudanar da zaben raba gardama don sauya kundin tsarin mulki.
Kuma an bijiro da irin wadannan bukatun a Jamaica, sannan da ire-irensu a New Zealand.
Kasancewa a kungiyar kasashen rainon Birtaniya ta Commonwealth sa-kai ne, kuma wasu kasashen da ke nahiyar Asiya yankin Pacific, ta yiwu su yanke matsaya wajen ficewa dungurungum, inda za su dumfari sababbin al'amuran harkokin rayuwa masu tasiri, kodayake kada kuri'ar Birtaniya na ficewa daga Tarayyar Turai na iya bai wa kasar damar kulla kawance da tsofaffin kawayenta na da.
Ba a dai bijiro da irin wadannan tambayoyin ba, game da Elizabeth II kan matsayinta a kungiyar kasashen Comonweath.
Fatanta da na iyalanta kamar yadda ta taba furtawa - "Karfin warwarar matsala na tattare da hakuri da juna da abokantaka da nuna kauna" al'amarin da in aka bijiro da su za su yi tasirin juya akalar harkokin duniya.
©Dukkan hotunan na da hakkin mallaka