Imran Khan 'ya ayyana' kansa wanda ya ci zaben Pakistan

Asalin hoton, AFP
Tsohon dan wasan kurket Imran Khan ya yi ikirarin cewa ya lashe zaben kasar Pakistan a yayin da 'yan hamayya ke zarginsa da tafka magudi a zaben.
A wata sanarwa da ya yi a gidan talbijin, ya ce: "Mun yi nasara kuma an ba mu dama."
Sai dai zuwa yanzu ba a sanar da sakamakon zaben ba a hukumance.
Amma sakamakon farko na zabukan ya nuna cewa Mista Khan na kan hanyarsa ta zama Firai Minista.
Yayin da rabin kuri'u ne aka kirga na zaben Majalisar dokokin da aka yi a ranar Laraba, jam'iyyar PTI ta Mr Khan ce take kan gaba.
Ana ganin ba za ta samu rinjaye ba kuma za ta nemi kulla kawance da wasu jam'iyyu. Jami'ai sun musanta zargin magudin zabe da abokan hamayyar Mr Khan suka yi.
An samu tashe-tashen hankula a yakin neman zaben da aka yi.
Mutum 31 ne suka hallaka a ranar zabe lokacin da wani bam ya tashi.
Mr Khan, mutum ne mai kwarjini wanda ya jagoranci kasarsa Pakistan a gasar wasan kurket ta duniya a 1992, amma tun da dadewa ya yi watsi da rayuwarsa ta fitattacen dan wasa kuma a baya-baya nan ana zargin sojojn kasar da mara masa baya a zaben.
Yayin da aka kirga kashi 49 na kuri'u, jam'iyyar Tehreek-i-Insaf (PTI) ta Mr Khan ita ce a kan gaba inda ta lashe kujeru 119 daga cikin 272 da ake da su a Majalisar dokoki, in ji jaridar Dawn Newspaper ta kasar, inda ta ambato alkaluman hukumar zabe ta kasar.
Kujeru 137 ake bukata domin jam'iyya ta samu rinjaye.

Asalin hoton, Reuters
Wannan dai shi ne karo na biyu da wata gwamnatin farar hula za ta mika mulki ga wata gwamnati bayan kamalla wa'adin mulki a Pakistan.
Sai dai jam'iyyar tsohon Firai Ministan Nawaz Sharif ta yi watsi da sakamakon zaben kamar sauran kananan jam'iyyu, wadanda duk sun yi zargin arigizon kuri'u.
"Yadda aka ci fuskar masu zabe, ba daidai ba ne," in ji Shehbaz Sharif, jagoran jam'iyyar Muslim League-Nawaz (PML-N) kuma kanin tsohon Firai Ministan kasar.

Asalin hoton, EPA
Shin wanene Imran Khan?
- A baya shahararen dan wasan kurket ne da ya jagoranci Pakistan a gasar wasan kurket ta duniya a 1992
- A Jami'ar Oxford ya yi karatu
- Ya rika jan hankalin kafofin watsa labarai saboda rayuwarsa ta fitattacen dan wasa kuma sau uku ya yi aure
- A 1996 ya kafa jam'iyyarsa ta Tehreek-e-Insaf (PTI) sai dai ya shafe shekaru yana siyasa
- Ya rika fafitukar yaki da cin hanci da rashawa da kuma siyasa ta gado a Pakistan
- Yana fuskantar tuhume-tuhume - zargin da ya musanta - a kan cewa sojoji kasar na taimakawa jam'iyyarsa.










