'Muna son a karrama Kudirat Abiola' - APC

An wallafa

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari, game da matakin da ya dauka na karrama marigayi Cif Moshood Abiola da lambar girmamawa ta GCFR.

Sai dai jam'iyyar ta yi kira ga shugaban kasar a kan ya karrama matar Abiola wato Kudirat Abiola wadda suka yi fafituka tare da mijinta.

A cikin sanarwar da jam'iyyar ta fitar mai dauke da sa hannun jami'in hulda da jama'a Bolaji Abdullahi, APC ta ce Kudirat Abiola ta rasa ranta ne a fafitukar da ta rika yi domin ganin an ranstar da mjinta a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasa na 1993.

"Ta cancanci a karramata saboda ta nuna jarumta kuma ta sadaukar da rayuwarta domin tabbatar da dorewar mulkin dimukradiyya" in ji APC.

"Ba mu manta da yadda marigayiyar ta rika tara mata 'yan kasuwa da masu fafituka da kuma dalibai wajen nuna adawa da mulkin soji ba."

A ranar 4 ga watan Yuni na 1996 aka kasheta a birnin Lagos.

A ranar Laraba ce Shugaba Buhari ya sanar da cewa gwamnatinsa za ta karrama marigayin Cif Abilola da kuma Babagana Kingibe, wanda ya tsaya a matsayin mataimakin shugaban kasa.

Shugaba Buhari ya kuma bayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimukradiyya daga badi.

Sai dai matakin na ci gaba da janyo ka-ce-na-ce a kasar.