Za a yi gwanjon biskit din jirgin yakin Trafalgar da ya shekara 200

An wallafa

Za a yi gwanjon biskit da ya rage a lokacin yakin Trafalgar wanda aka yi fiye da shekara 200 da ta wuce.

An yi amanna cewa, biskit din wanda mallakar daya daga cikin ma'aikatan wani jirgin ruwan ne, mai suna HMS, na daga cikin biskit mafi dadewa a duniya.

An yi zaton cewa an kai biskit din gidan adana kayan tarihi a Denmark a shekarar 1852.

Wanda zai jagoranci gwanjon biskit din, Oliver Pepys, ya ce abin a tuna ne da wannan biskit, kuma bai taba ganin biskit da ya jima kuma yake da kyawun gani kamarsa ba.

Thomas Fletcher, shi ne ainihin mutumin da ya sayi biskit din ya shiga da shi jirgin domin ya rinka hada shi da shayi yana ci.

Iyalan Mista Fletcher ne suka adana biskit din har zuwa shekarar 2005, daga bisani suka yi wa wani mutum gwanjonsa.

Yanzu haka dai za a yi gwanjon tsohon biskit din da ma wadansu kayan Mista Fletcher.

Ana kyautata zaton za a yi gwanjon biskit din a kan kudi fam 2000 zuwa 2,600 ( kimanin naira miliyan daya), a ranakun 9 da 10 ga watan Mayu masu zuwa.

Mista Pepsy ya ce, ba mamaki kudin da za a sayi biskit din ma ya zarta wanda ake sanya ma sa.

Yakin Trafalgar yaki ne da aka yi a 1805 tsakanin sojojin ruwan Birtaniya da kuma na Faransa tare da goyon bayan sojojin ruwan Spain

Yakin shi ya kawo karshen mulkin sarkin Faransa Napoleon Bonaparte, wanda ya shirya mamaye kasar Ingila.

An kashe shahararrun mutane a yakin, ciki har da Vice Admiral Lord Nelson.

Karanta wadansu karin labarai