Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Taliban na barazanar mamaye kashi 70 cikin 100 na Afghanistan
- Marubuci, Daga Shoaib Sharifi da Louise Adamou
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service, Kabul
- An wallafa
Wani bincike da BBC ta gudanar ya gano cewa mayakan Taliban, wadanda dakarun da Amurka ta kashe makudan kudi don murkushe su, a yanzu haka sun dawo da karfinsu inda suke barazanar mamaye kashi 70 cikin 100 ma kasar.
Watannin da aka shafe ana bincike a fadin kasar ya nuna cewa a yanzu haka Taliban ke iko da ko kima take barazanar mamaye yankuna da dama fiye da lokacin da dakarun kasashen waje suka bar kasar a 2014.
Gwamnatin Afghanistan ta ce rahoton ba abun da za a damu a kansa ba ne, saboda tana iko da yawancin yankunan kasar.
Amma wasu hare-hare da aka kai a baya-bayan, wadanda kungiyoyin Taliban da IS, suka yi ikirarin kai wa sun yi sanadin mutuwar mutane da dama a birnin Kabul da ma wasu wuraren.
Jami'an gwamnatin Afghanistan da Shugaba Donald Trump na Afirka, sun mayar da martani ta hanyar kawar da yiwuwar yin duk wata tattaunawa da Taliban.
A shekarar da ta gabata ne, Mista Trump ya sanar da cewa dakarun Amurka za su ci gaba da zama a kasar har sai baba ta gani.
Binciken BBC din ya kuma gano cewa kungiyar IS ta fi karfi sosai yanzu a Afghanistan fiye da baya, duk da cewa dai karfinta bai kai na Taliban ba.
Yankuna nawa ke karkashin ikon Taliban?
Binciken na BBC ya nuna cewa a yanzu Taliban suna da cikakken iko da gundumomi 13, wato kashi 4 cikin 100 na kasar kenan.
Kusan mutum miliyan 15 - rabin al'ummar kasar -su na rayuwa a yankunan da ko dai suna karkashin ikon Taliban ko kuma Taliban din na kai hare-haerenta a bayyane.
Wani mutum mai suna Sardar da ke zaune a Sardar na gundumar Shindand da ke yammacin kasar, wanda ke fama da hare-haren Taliban duk mako ya ce, "A duk lokacin da na bar gida ba ni da tabbas din cewa zan koma gida a raye."
Binciken BBC din ya nuna cewa a bayyane yake yanzu Taliban ba a yankin kudancin kasar da a da shi kadai ke karkashin ikonsu kawai suke ba, sun kara dannawa har gabashi da yammaci da arewacin kasar.
Yankunan da suka koma karkashin ikon Taliban tun shekarar 2014 sun hada da na gundumar Helmand irin su Sangin da Musa Qala da Nad-e Ali, amma dakarun kasashen waje sun yi kokarin dawo da su karkashin ikon gwamnati, al'amarin da ya sa Taliban ta rasa karfinta a 2001.
Fiye da sojojin Birtaniya 450 ne suka mutu a Helmand a tsakanin 2001 zuwa 2014.
Su waye 'yan Taliban?
- Kungiya ce mai da'awar kafa daular musulunci da ta fara ayyukanta a shekarar 1998 a Afghanistan in 1996, bayan yakin basasar da ya biyo bayan yakin da aka yi tsakanin tsohuwar tarayyar Soviet da Afghanistan, amma rundunar sojin da Amurka ta jagoranta sun tumbuke su shekara biyar bayan nan
- A lokacin da suke da karfi, sun kaddamar da abun da suka kira tsarin Shari'a kamar kashe mutane masu laifi a bainar jama'a da yanke musu hannaye da haramtawa mata fita bainar jama'a
- Sun tilastawa maza tsayar da gemu da kuma sa mata rufe jikinsu ruf da hijabi da nikabi; sun kuma haramta kallon talbijin, kida da waka da kuma zuwa sinima
- Sun bai wa shugabannin al-Qaeda mafaka kafin da kuma bayan an kore su - tun daga lokacin suke yakin da ake zubar da jini har zuwa yau
- A shekarar 2016, yawan fararen hular da suka jikkata a Afghanistan ya karu - al'amarin da Majalisar Dinkin Duniya ta dora alhakinsa a kan Taliban