Dokar kare sirrin bayanai ta BBC

An wallafa

Amincewar da kuka yi mana na da matukar muhimmancin a wurinmu. BBC ta kudirin aniyyar kare dukkan bayanan da suka shafe ku, a duk lokacin da kuke hulda da wasu abubuwa na BBC.

Yana da matukar muhimmanci ku karanta wadannan bayanai domin sani yadda za mu yi mu'amula da bayananku.

Wannan dokar ta kare sirrin bayanan na bayyana yadda za mu karbi bayananku da kuma yadda za mu yi amfani da bayanan a lokaci da kuma bayan huldarmu da ku, bisa doron dokar kare bayanan sirri.

Dalilin gasar wakar da yadda za ku shiga tsarin

Sashen Hausa na BBC na watsa shirye-shiryensa ga jama'ar da ke Magana da harshen Hausa fiye da miliyan 20 a fadin duniya - ta hanyar rediyo da intanet da talbijin da kuma soshiyal midiya.

Kasancewar sashen na BBC Hausa ya cika shekara 65 da kafuwa, a 2022, ya sa muka bude wannan gasar ta waka domin wake sashen.

Sashen Hausa na BBC ya ba ku damar baje kolin fasahar da Allah ya huwace muku ta waka. Muna son jin wakoki masu dauke da kida da amsa-amo a harshen Hausa.

Za a aike da wakar ne ta shafinmu na bbchausa.com, inda za a cike fom kuma a aika da wakar a tsarin sauti na MP3.

Abubuwan da za a duba a wakokin sun hada da yadda aka gina wakar a kan turke da kida da amsa-amo da sauran tubalan wakar da suka dace da turke.

BBC za ta zabi wakokin da suka yi fice guda 30 daga cikin gommai ko daruruwan da aka aiko, bisa mizanin tantance wakokokin domin mika wa alkalan gasar.

Ba za a bari alkalan su fahimci wanda ya yi kowace waka ba. Alkalan gasar za su zabi wakoki 3 da suka zamo zakara sannan kuma da karin 12 wadanda suka cancanci yabo amma ba su yi nasara ba.

Ukun da suka yi nasara za su karbi tukwicin dalar Amurka, inda ta daya za ta karbi kyautar $3,000, biyu kuma ta samu $2,000 sannan ta uku ta karbi $1,500.

BBC za ta yi amfani da wakokin da suka zamo zakaru guda uku ta hanyar watsawa a rediyo da intanet da soshiyal midiya da twitter da Instagram da Facebook.

Idan aka watsa wadannan wakoki naku za su iya zama har abada a shafukan BBC na intanet ko kuma a sake amfani da wakokin naku a nan gaba idan bukatar hakan ta taso.

Akwai yiwuwar BBC za ta gayyaci zakarun uku da watakila wasu daban domin halartar bikin mika kyautukan a Abuja, babban birnin Nijeriya (idan annobar korona ta bari).

BBC za ta kama wa wadanda aka tuntuba din wurin kwana da kudin sufuri. To sai dai duk wanda aka gayyata wanda yake bukatar biza, to sai dai ya nema wa kansa.

Ma'aikatan BBC Hausa za su karbi bayananku a lokacin da kuka shiga gasar ta waka ta 2022. Za kuma a karbi wadannan bayanan ne ta kafar intanet.

Yana da kyau a karanta ka'idojin shigar gasar a nutse kafin aike wa da waka.

Domin sanin yadda BBC za ta yi amfani da bayananku a lokacin da kuke hulda da ita, ku duba yadda muke kare bayananku na sirri a nan.  

Wadanne irin bayanai ne BBC za nema a wurinka sannan yaya za ta yi amfani da su?

BBC za ta karbi bayananku ta kuma yi amfani da su. Dole ne a aiko da bayanan ta hanyar shafin BBC na intanet sannan dole ya kunshi wadannan abubuwa da suka shafi mai aiko da waka:

•Cikakken suna

•Kasar da mutum yake

•Adireshin Imel

•Lambar waya

•Waka (a tsarin MP3)

Idan ka/kin kasance zakara, za mu nemi lambar asusu domin sanya kyautar a ciki.

Ba za a mayar wa mutum wakar da ya aike da it aba saboda haka ya kamata a ce mutum yana da kwafin wakar. Ba za a tuntubi wadanda ba su yi nasara ba sannan ka da su tsamamci za a yi musu bayani dalilin da ya ba su yi nasara ba.

Wake lura da bayananku na sirri?

BBC c eke sarrafa bayananku na sirri. Hakan na nufin BBC ce ke yanke hukuncin kan yadda ya kamata a yi amfani da bayanan naku. Domin gudun zargi, za a karbi bayanan naku ne kawai domin amfani da su kamar yadda aka tsara a wannan dokar ta bayanan sirri.

Amfani da bayananku ta hanyar da ya dace

Dokar da BBC ta dogara kai dangane da amfani da bayananku ita ce dokar da ta gindaya wa BBC kare 'yancin jama'a. Aikin BBC shi ne ilmantarwa da nishadantarwa da kuma sanar da jama'a ta hanyar ba su bayanai masu inganci kuma na daban.

Domin cimma hakan dokar da ta kafa BBC ta ce dole ne BBC ta samar da bayanai masu inganci ga jama'a. Bayanan kuwa ka iya zama a kowane bangaren rayuwa sannan ta kafofi daban-daban a Burtaniya ko kuma sauran kasashen duniya.

Bai wa wasu bayananku na sirri

BBC na aiki da wasu abokan huldar daban da ke taimaka mata cimma burinta na samar da bayanai. Wadannan abokan huldar za su iya yin amfani da bayananku ne kawai da iznin BBC ba wai su yi gaban kansu ba.

Za a mika wa alkalan gasar bayananku.

Sauran gidajen rediyo da talbijin da suke hulda da mu ka iya amfani da wakokin naku.

Akwai yiwuwar mu iya bai wa wasu abokan huldar tamu bayanan naku amma bisa doron doka.

Har zuwa yaushe BBC za ta rike bayanan naku?

Idan har wakokinku ba su yi nasara ba, to BBC za ta rike bayananku da abin da kuka aiko mata har zuwa ranar 14 ga watan Agustan 2022.

Ga kuma wadanda suka yi nasara, to za mu ajiye bayananku har zuwa shekaru biyu bayan gasar.

Idan kuma aka yi amfani da wakokin naku a kafafen watsa labarai, to bayanan naku za su ci gaba da kasancewa da BBC sannan za a taskace su har abada.

Bayanan da kuka aika ta hanyar fom zai za a taskace shi a Burtaniya da EEA.

Wadanda kuma aka tuntube su da wadanda suka yi nasara, bayanan nasu zai kasance a Nijeriya. Ko Burtaniya ko Nijeriya, BBC za ta tabbatar da ta kare hakkinku na bayanan sirri bisa doron doka.

Abin da ya kamata ku sani kan hakkin bayanan sirrinku

Kuna da 'yanci a dokar kare bayanan sirri.

Za ku iya neman kwafi na bayananku da BBC ta taskace.

Kuna da 'yancin ku nemi BBC ta goge bayananku da muka karba duk da cewa akwai iya hurumin da kuke da shi domin BBC ka iya kin biya muku bukatar taku.

A wasu lokutan ma kuna da damar takaita ko kalubalantar yadda za a yi da bayanan naku.

Kuna kuma da 'yancin neman mu bai wa wasu kungiyoyin bayanan naku, idan bukatar hakan ta taso.

Za ku iya tuntubar , Data Protection Officer a duk lokacin da kuke son sanin damarmakin da doka ta ba ku dangane da bayananku da ke hannunmu. Za kuma ku iya ziyartar shafinmu na http://www.bbc.co.uk/privacy.

Idan akwai abin da ba ku fahimta ba dangane da yadda BBC take rike da bayananku na sirri za ku iya daga maganar zuwa hukumar da ke kula da bayanan jama'a na sirri ta Burtaniya ta hanyar ofishin Kwamishinan kula da bayanai https://ico.org.uk/.

Sake sabunta dokar bayanan sirri

Za mu yi wa dokar bayanan sirri kwakwarima idan har akwai wasu manya sauye-sauye dangane da yadda muke amfani da bayananku na sirri.